Search
Subscribe
Nasiha zuwa ga maza (11)

Nasiha zuwa ga maza (11)

Ba wadannan kadai ba, muna da Hajiya Hajjo Haja, ita ma a halin da muke ciki zaune take ita kadai ba aure, domin ta yi aure uku, abin ya ki, saboda kurum ta tsaya kai-da-fata za ta ci gaba da sana’arta ta sayar da haja, wadda Allah Ya sa mata so da gwanancewa tun tana makarantar sakandare. Ba abin da Hajjo ta iya irin sayi wannan, sayar a cikin unguwa. Kamo wancan, sayar a tsakanin ’yan uwanta mata a makarantar kwana da ta yi. Ko kafin ta kammala karatun sakandare an san ta da kokarin sayar da haja. ’Yan kunne da takalman mata da zannunwa da rigunan mata da kayan kwalliya na mata iri-iri, ta gwanance kan haka. Saboda haka ko da aka aurar da ita tana da shekara 18 ba ta bar wannan sana’a ba, sai dai ita ce ta kasance matsalolin rayuwarta da aurarrakin da ta yi a baya.

A kullum abin da take bayyana mana in mun kai mata ziyara shi ne, ‘wai mene ne matsalar? Shi namiji Bahaushe bai iya auren mace mai sana’a ko ilimi ko wani da ta dogara a kansa? Shi ke nan ita matar Bahaushe sai dai ta tsaya hannu-miji, ba hannu-rabbana ba, koda Rabbana Ya ba ta wata hanyar da za ta rufa wa kanta asiri da na iyalinta? Ita matar Bahaushe ba ta da damar da za ta dama cikin arziki ko dukiya ko fita cikin kangin bauta da talauci?

Ba wani abin ban takaici game da rayuwar Hajjo Haja sai yadda ta rika shan kwaramniya da mijinta game da sana’arta ta sayar da haja. A kullum maigidanta ya dawo gida ya ga mata zaune a falo, an baje haja ana ta hada-hadar saye da sayarwa, ana mika kudi, tana amsa tana zubawa cikin jaka ko kaiwa kuryar daki, ransa ba so yake yi ba. Tun yana gyarar murya a san yana cikin gida, sai ya kai ga murtuke fuska da bata rai; kai da gani ka san cewa abin da ke wakana a cikin gidansa, bai faranta masa rai. A kullum rana ta Allah sai sun gardance shi da ita game da yadda ake cika masa gida da mutane, shi ke nan kullum kokawa, yana cewa ‘mutum bai da ikon ya dawo gida ya huta sai hayaniyar mutane, kamar ba gidanka ba.’ Wannan fa duk saboda samun da Hajjo Haja ke yi ne daga sana’arta, a cikin gidanta, a dakin mijinta, ba wai a kasuwa ba! Ba kuma wai ba ta taimakawa ga harkokin gidan ba ne daga ribar da take samu, ko alama! Cefane kusan ita ce ke yi. Kayan Sallar yara duka, ita ce mai saye da dinkawa. Ba a maganar nata kayan, wata sa’a har da na maigidan. Amma kullum ba ya komai sai jefa magana da shagube da nuna rashin godiya, duk don Hajjo Haja ta samu abin rufin asiri!

Bisa wannan matsaloli ne auren ya rabu, Hajjo Haja ta sake auren wani da ya yi alkawarin barinta ta ci gaba da sana’arta, amma a shagon da ta kama a wajen gidan. Shi ma ba a dade ba suka babe, ya ce ya gaji yadda yake ganin karti na kai-kawo shagon, wai sun zo sayayya. Daga karshe da tsegumin ya yi yawa, suka rabu, ta sake wani auren, amma wannan karon ta tare a cikin gidanta, ta ci gaba da sana’arta, duk kuwa da cewa makwabta na ta zungurar mijin da maganganu marasa dadin ji, ya daure haka nan, har yanzu suna gungurawa.

A nan ne wasikar ta kawo karshe, sai wannan mata ta ce da ni ba tare da ta ba ni lokacin da in kara nazartar zantuttukan da matan suka zo da su ba, ta ce, ‘yanzu daga wadannan bayanai Malam, sai a ce laifin na matan ne ba na mazan ba? Shin mene ne laifin matan a nan? Yaya ake so su yi? Shin aure bautar Allah ce ko bautar namiji? Shin wa ke bukatar taimako tsakanin namiji Bahaushe ko matar Bahaushe?

Ba ta jira na ba ta amsa ba sai ta ci gaba da cewa, ‘ba wanda ke bukatar taimako irin namiji Bahaushe. Shi ke aura, shi ya kamata ya ja ragama, amma ya kasance mai daidaitawa bisa tsari da aminci da yarda. Amma Malam haka batun yake?’

Ban dai amsa mata ba, sai da na tabbata ta kai karshe, inda take cewa, ‘na tsokano wadannan batutuwa ne ba wai don na san za ka iya bayar da amsa bisa kan kowane tsokaci ba, sai dai don na san za ka iya dora ni bisa hanya da za ta kai ni tudun-mun-tsira! Fatata ita ce mu tattauna da kai da ni da duk wadansu masu karatu domin a ga inda gizo ke sakar, a kuma duba ko sakar ba da mataccen zare ake yi ba, yaya kuma za a iya warware zare da abawa. Ka yi min afuwa in har na wuce gona-da-iri, ba yadda zan yi ne, abubuwa ne da suka dade suna ci mini tuwo a kwarya, dole ta sa na yarfe su a nan. A yi min aikin gafara! Na gode’

Sai da na yi kwana uku ban sake komawa cikin akwatin ajiye sakona ba, domin kuwa na san tattaunawar ta zo karshe, ga shi kuma ban san ta inda zan soma ba ta amsa ba. Ba kuma don ban da amsar ba ne, sai dai ganin cewa ta kwaso batutuwa da suke masu kama da juna, amma kuma mabambanta. Masu shiga zuci, kuma masu daukar hankali. Masu harzukawa, kuma suna iya tunzurawa. Masu gaskiya da kuma masu yawan hasashe. Masu sosawa da kuma sasantawa. Duk da haka ranar nan sai na leka akwatin nawa, ba kuwa abin da na ci karo da shi face sakonta na nuna damuwa da alhini, ta ce a cikin sakon. ‘Ina fata Malam ba fushi ya yi da mai neman karuwa daga gare shi ba?’

Nan take na maida martani na ce da ita, ‘ko alama nazari nake ta yi, ki saurari nawa tunanin nan gaba kadan mai taken ‘Mazan ne ko matan a tsakanin Hausawa!’ Na gode da haduwa da ke a wannan hauji.

Mun kamala

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin