Search
Subscribe
Nasiha zuwa ga maza (4)

Nasiha zuwa ga maza (4)

Na tabbata in aka yi haka, to kila abin da ya faru ga irin su Maryam da Halima da Indo ‘A’i da Hajara da Kande da Lami da wadansu da dama da bai same su ba a tsawon rayuwa. Aure bautar Ubangiji ne ya kamata ya zama Malam, ba BAUTA ba!

A lokacin da na kawo kan wannan gaba na bayananta, abubuwa da dama suka shigo mini cikin rayuwa.

1. Na farko dai, bisa ga dukkan alamu wannan mata, mace ce mai son ganin ’yan uwanta mata sun samu damar da za su kasance cikakku daga cikin halitta, ko kuma su daga daga wani matsayi da suke, wanda take ganin bai ishe su ba, zuwa ga wani da take ganin shi ne mafi a’ala.

2. Na biyu, daga amon kalamanta kuma na fahimci cewa ta ga duniya ko dai ta zahiri ko ta makaranta, domin kuwa bayananta na nuna mini cewa tana da abubuwan fada game da rayuwar mata, kila har da misalai.

3. Na uku kuma shi ne, akwai wani abu da take son ta gaya mini, amma take noke-noke, ko tana tsoron irin yadda zan kalle ta bayan ta amaye.

Ganin cewa turakar da muke wannan zance tawa ce, ba kuma wanda ya san abin da ke wakana daga ni sai ita, ba kuma wasu sharudda da aka gindaya game da abin da za mu fada wa juna, ya sa na koma baya domin tabbatar da ina muka nufa daga nan.

Zama na yi na tura mata sako cikin dare ina cewa, duk da ban san ko da wa nake zance ba, domin a bangon gidanki ba hoto, na shiga cikin dakin naki kuma ban ga wani jawabi da ya nuna mini ko ke wace ce ba, sa’annan ga shi ba ki bayyana ko ma macen ba ce ko namiji, amma na biye maki ne, a matsayin mace, ba don komai ba sai don fagen na ilimi ne, fage ne na karuwa da juna, daga namiji ko mace ko kuma daga wa ma! In kin lura ina dari-dari wajen amsa ba ki da fadada bayanai saboda rashin sanin tabbas, amma idan ba ki damu ba, me zai hana a bayyana kai, sai mu yi keke-da-keke, don ban yarda da wasu bayanan naki ba.

Ba a ko dade ba ta maido da amsa, tana cewa ‘wallahi Malam ba dodorido nake maka ba, ina biye da kai da sauran abokai na facebook da dadewa, ka san yadda lamuran suke ne, bayyana a fili na iya kawo matsala, gare ka ko ni, musamman ma ni. Kuma sai na ga bayyana kai bai karawa ko ragewa bisa ga ilimin da muke musaya. Ni fatata ita ce in karu, in kuma karar da kai da kuma dimbin dalibanka da ke biye da kai a kullum da kuma masoyanka a duniyar facebook, kila ta haka a samu canji a tunani ko zahiri game da yadda muke daukar lamuran karatu da ayyukan mata a wannan zamani. Duk abin da na fada da wanda zan karasa zuwa gobe insha Allah, gaskiya ce ko dai daga zuciyata da karatuna da kuma abin da ya faru a zahiri. Wallahi Malam kana iya kararwa, ni a tawa fahimta, yawancin matan Hausawa ba bautar aure suke yi ba, bauta ce irin ta tsakanin wanda aka fi karfi a tsakanin ’yan Adam.’

A cikin daren nan na koma farkon farawa a cikin akwatin sakona na kwashe duk abin da ta turo min da amsoshin da na ba ta, na zube a akwatin tattara bayanaina cikin kwanfutata domin tanadin gobe. Na san zan bukaci wadannan bayanai nan gaba.

Kammala haka ke da wuya sai na lalube ta, amma ban ji motsinta ba, na ce a raina kila ta yi barci, sai na tura sakon da ke cewa ‘wa ke bautar da matan da kike ikirari, me kuma ya faru ga su Maryam da Halima da Indo ‘A’i da Hajara da Kande da Lami? Zan so in ji ko ma karu?’

A cikin kwanakin da muka yi muna tattaunawa, wannan shi ne karo na farko da na kosu da ganin amsar wannan baiwar Allah, domin kuwa da alama nan ne ruhin zancen nata yake, kuma ni ma ina da masaniyar cewa in da a fili ake wannan tattaunawa to da kila yanzu an yi mata ca, ganin cewa ba kowa ne ke jure tunani na kamfen din sama wa mata wata sabuwar rayuwa daga wadda suke ciki ba. Sa’annan batun inganta rayuwar mata a tsakanin Hausawa a kan lullube shi da mahanga masu yawa da yawanci ba haka ya kamata su kasance ba.

Tunda safe na bude akwatin sakona, shiru. Ina ofis ina aiki, nakan leka ko akwai sakonta, ba labari. Can na kammala Sallar La’asar, na shiga sai ga sakon nata, tana cewa; ‘A yi mini aikin gafara game da batutuwan da zan fada yanzu da kuma nan gaba. Na san za ka fahimta, ba turjiya da neman tashin-tashina ba ce, ni yadda na kalli lamuran ne. Tana yiwuwa ban kalle su da kyau ba, amma ina da yakinin abin da ke faruwa a cikin yawancin gidajen mazan Hausawa dangane da mata ko addini bai amince da shi ba, ana dai shiga cikin rigar addini ne, amma da alama al’adu da son rai da daure gindin hukuma, su ne ke kara tabbatar da wannan matsayi da mata ke ciki. Addini cewa ya yi a yi aure domin a samu abubuwa guda uku.

1. Natsuwa tsakanin namiji da mace.

2. Samar da iyali da kuma kintsa iyalin da tabbatar da iyalin bisa tafarkin da ya dace.

3. A samu haihuwa domin ci gaban gudanuwar al’umma da kuma kasancewa abin alfahari a ranar tashin Kiyama.

Ta ci gaba cewa ‘Allah Ya gafarta ni a tawa fahimtar da nazarin da na yi, sai na ga kusan dukkan wadannan batutuwa uku da wasu irinsu a baibai ake gudanar da su a tsakanin Hausawa, musamman ta inda ya shafi mata.

Za mu ci gaba

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin