✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nasiha zuwa ga maza (5)

Ta ci gaba cewa ‘Allah Ya gafarta, ni a tawa fahimtar da nazarin da na yi, sai na ga kusan dukkan wadannan batutuwa uku da…

Ta ci gaba cewa ‘Allah Ya gafarta, ni a tawa fahimtar da nazarin da na yi, sai na ga kusan dukkan wadannan batutuwa uku da wasu irinsu a baibai ake gudanar da su a tsakanin Hausawa, musamman ta inda ya shafi mata.

Idan ka tambayi yawancin mata za su ce da kai, natsuwar da ake bukata a samu tsakanin namiji da mace idan an yi aure, yawanci tana ga namiji ne. Shi ba abin da yake bukata irin in dai ya shigo gida ya gan ta, ta sha kwalliya, tana sheki, abin sha’awa, to ta yi abin da addini ya ce, ta sa masa natsuwa. In kuma dare ya yi, ya biya bukata, shi ke nan, ya samu wata karin natsuwar.

Yawancin mazan Hausawa ba su damu da sanin ko ita matar ta samu natsuwar ba. Ba ruwan yawancin mazan Hausawa da yin kwalliya ko kasancewa cikin sheki domin matansu su samu natsuwa da su a cikin gida, su ma. Idan ka ga mazan Hausawa sun yi kwalliya to yawanci ba don matan suke yi ba. Kwalliya da sheki ga namijin Bahaushe, domin mutanen waje ne ba na matansu ba. A yawancin lokuta namijin Bahaushe, sai zai fita yake cakewa, in ya dawo gida kuma ya kasance tamkar bawa, ba sheki ko annuri domin matansa!

Idan kuma muka koma batun rayuwar dare kuwa, Malam nan ma, sai  dai a hankali. Na sha hira da ’yan uwana mata da suke nuna min cewa ba su fahimci natsuwar da ake magana ba in an yi aure, musamman in dare ya yi. Sukan yi min tambaya, raba kwana shi ne natsuwar? Ko kwanciyar daren? Ko ko me? Akwai wadda take fada min ita dai tana ganin ’ya’ya na fita ne daga jikinta, amma ba don tana samun natsuwa da mijin nata ba a kowane hali. Ta ce a dukkan haihuwar da suka yi, minti 30 yake yi a cikin dakinta a cikin dare, da sun kare, ya sabi rigarsa ya koma turaka, ya bar ta kwance, ta rasa inda ke mata ciwo. Akwai kuma wadda ke gaya min cewa, ita turakar take bin sa, da zarar ya natsu shi ke nan, sai ya shiga barci da minshari, tana kwance tana kallonsa, ita kuma tana kume cikin damuwa, ‘ba ta san irin bam din da ya fada mata ba,’ haka za ta ja jiki ta koma dakinta cikin taraddadi.

“Malam na bude maka wannan wagar ce domin mu muka san halin da muke ciki, shi ya sa yanzu na yarda da fadar nan da ake cewa ‘ciwon ’ya mace, na mace ce,’ yawancin mazan Hausawa ba za su taba ganewa ba!

Mu koma kan batun ana yin aure domin a samar da iyali da kuma kintsa iyalin da tabbatar da iyalin bisa tafarkin da ya dace. Nan ma akwai wagegen gibi da ya dace mu yi la’akari da shi. Ta ce haihuwa na daya daga cikin kyautar da aure ke samarwa, sai dai ni a tawa fahimtar ba haihuwar yuyuyu ya dace ana yi ba, a samar da ’ya’ya, kwarara. Amma me muke gani a halin yanzu a cikin al’ummar Hausawa, a gidajen mazan Hausawa? Alhamdulillah, Allah Ya huwace mana zuriya ba sai an nanata ba, amma wace irin koyarwa muke yi wa yawancin abin da muka haifa? Wace irin tarbiyya muke ba wadannan yara da muka haifa? Shin haihuwar ce abin alfahari ko kuwa tarbiyantarwar ce abin godo a wannan yanayi? Daga dan karatun da na yi, na ga cewa akwai almajirai da yaran da ba su san inda za su samu abincin yau, bare na gobe sama da miliyan 11 da suke gararamba a tituna da gidajen masu hannu da shuni da gidajen karuwai da sauran wuraren da ba gidajen iyayensu ba. ’Ya’yan nan daga ina suke fitowa, yawancinsu daga gidajen Hausawa suka tuzgo, ba kula, ba damuwa, ba kuma abin da wadansu za su iya yi game da haka. Wannan shi ne samar da iyali da kuma kintsa iyalin da tabbatar da iyalin bisa tafarkin da ya dace? Wane tafarki ke nan muke dora wadannan ’ya’ya namu, kuma laifin daga ina ya taso? Kamar yadda na sha fada Malam a tattaunawar da muka yi can baya, irin rigunan da matan Hausawa ke sanyawa a baibai ke jawo haka.

Idan da mun bar matan Hausawa suna sanya rigunan karatu da sana’ar yi ta kwarai da mun rage wannan kwamacala. Na san ka sani Malam, yawancin matan Hausawa suna aure da wuri, kamar yadda wani bincike da na gani ya nuna, kashi 5 cikin 100 suna aure kafin shekara 14, kashi 20 cikin 100 kafin shekara 19, sa’annan kashi 39 cikin 100 kafin shekara 24. Yawancin wadanda suka yi auren kuma Malam ba dadewa, sai ka ga sun kasance zawarawa, su komo gida su gauraya da wadanda ba su yi auren ba, a koma ’yar gidan jiya. Shi ya sa bayan miliyoyin yara kanana da ke galudiya a tsakanin al’ummar Hausawa abu na gaba shi ne mutuwar aure da yaduwar zawarawa, wanda dukkansu, matsaloli ne da suke da alaka da rigunan da matan Hausawa ke sawa a rayuwa.

Malam, ta yaya yarinyar da ba ta yi ilimin kwarai ba, ba ta samu horon da ya dace ba, ba ta samu kulawar da za ta amfane ta ba, za ta iya tarbiyyantar ko kula da wadansu? Ta yaya kananan yara za su kula da da kananan yara irin su? Shin wannan shi ne abin da muke kira da a yi aure a samu damar haihuwa domin ci gaban gudanuwar al’umma da kuma kasancewa abin alfahari a ranar tashin Kiyama? Almajiran da ba su san inda kan suke musu ciwo ba, me za su iya kawo wa al’umma don ciyar da ita gaba? Yaran da ke gararamba bisa titunansu ne za mu yi alfahari da su a nan? ’Yan mata, bila adadin da ke famar talla tun daga carar zakara har zuwa shigewar kyalla matsuguni su ne abin tokabo? Abin da yawa Malam!

Babu wata riga da matan Hausawa za su sa ta taimaka wajen kawo sauki ga irin wannan rayuwa irin ta zurfafa ko kaurara iliminsu na addini da na zamani. Rashin yin haka shi ne babban tarnakin da ke gaban hukuma da masu fada-a-ji. Rashin kula da aiwatar da tsare-tsare kan haka, na daga cikin abin da ya jefa su Maryam da Halima da Indo ‘A’i da Hajara da Kande da Lami da wadansu irinsu da dama cikin rayuwar jangwam! Labarinsu tamkar labarin yawancin matan Hausawa ne Malam!

Za mu ci gaba