✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nasiha zuwa ga maza (8)

Bayan kamar kwana biyu da wannan zance, ran nan sai na ga sakonta tana mai neman afuwa, ta ce, ‘na san Malam ya ji shiru…

Bayan kamar kwana biyu da wannan zance, ran nan sai na ga sakonta tana mai neman afuwa, ta ce, ‘na san Malam ya ji shiru daga gare ni, bulaguro na yi na aikin ofis, ban samu sukunin lekowa ba, amma insha Allah zuwa gobe zan turo maka wata wasikar da na samu daga Indo A’i da kawarta Hajara, ka ji su kuma taskun da suka shiga daga hannun mazan Hausawa da kuma illar rashin samun sanya wadancan tufafi da na yi maka bayani tun a farkon gamuwa.

A lokuta da dama ba na kula sakonnin da nake samu a cikin akwakun ajiye sakona na wannan kafa ta facebook, saboda tarin yawan sakonni a kowace rana ta Allah. A kullum sai na samu daruruwan sakonni, wasu daga dalibai suna neman a fasa musu wannan baki ko a sama musu mafita daga matsalolin yau da kullum, balle kuma uwa-uba masu aiko da gaisuwa, ta safe daban, ta rana daban, ta dare daban, ga kuma ’yan tsakar dare, yawanci biris nake yi, ko na ma ki bude akwakun domin in sarara. Amma a wannan karon a kullum rana ta Allah sai na leko akwatin ajiye sakonnin domin in ga abin da wannan mata ta turo mini, da kuma neman sanin yau ina ta nufa da batutuwan nata. Shi ya sa da ta ce mini zuwa gobe, na zaku goben ta yi inji kuma dawan da muka dosa, domin da gangan nake nokewa da yin nawa sharhin, don in ba ta dama ta amaye abin da ke cikin zuciyarta.

Sakon nata bai zo ba sai can bayan Sallar La’asar, kuma lokacin nan aiki ya rufe ni a ofis, ban leka akwatina a lokacin ba, sai can da dare da misalin karfe 11, na sauko da sakon nata, na fara karantawa.

Ta ce, “Kafin na zube maka wasikar su Indo A’i da Hajara, akwai wani abu da ban bayyana maka ba tunda farko, wato ina cikin wata kungiya ta musamman da muka kafa domin kokarin sama wa matan da ke cikin kunci saukin gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum daga ko dai mazan Hausawa suka dunguza su ciki ko kuma rashin sanya tufafin kwarai na gudanuwar rayuwa kamar yadda na lissafo can a baya ko kuma sakaci na hukuma da masu fada-a-ji na wannan kasa. Daga cikin aikin wannan kungiya akwai kokarin kididdige yawan matan da ke da damuwa kowace iri domin sanin irin tallafin da za mu iya ba su, ‘mu da muka hau tudun mun-tsira.’ Haka kuma muna zagayawa domin tattaunawa da su da kuma ba su gudunmawa. A wasu wuraren har makarantun manya na kore jahilci muka bude domin dora irin wadannan mata bisa sabuwar turba, haka kuma muna kokarin jawo hankalinsu da kada su kasance sun bar ’ya’yansu mata sun fada cikin tarkon da su suka samu kansu.

A bisa irin wannan tafarki ne muka ci karo da Indo A’i da kawarta Hajara, wadanda suka kasance zawarawa ne da suka yi shekaru ba su sake aure ba ko kuma ba su samu mazan da suka dace da su ba, domin suna da tabbai masu yawa a jikinsu na daga rayuwar yau da kullum daga zama da suka yi da mazan Hausawa. Bayan mun tattauna da su game da irin yadda muke ganin ya dace su gudanar da rayuwarsu, sai muka fahimci cewa kamar zancen namu bai shiga kunnuwansu ba. Sun nuna mana cewa su suna ganin ba su da wata mafita game da halin da suke ciki, domin kuwa an baro shiri tun rani. Mun yi iyakar yi domin mu nuna masu cewa akwai mafita ba a dai gwada ba, amma suka yi kemadagas. Sai daga baya lokacin da za mu wuce, suka dube mu suka ce, ‘ba wai mun ki jin ku ba ne da gangan, akwai dalili, kuma labarai ne masu tsawon gaske.’ Jin haka muka ce ai abin da muke so ke nan mu ji, su fada mana, mu ga inda za mu iya taimakawa. Sun dade suna tauna batun namu, daga baya Hajara ta ce, za su turo mana da sako ta tasha, idan ya zo, sai mu karanta mu ji halin da suke ciki, ba ma su kadai ba, tattare da sauran irinsu da ke wannan gari. Nan ne na tambaye su wa zai yi musu rubutun, sai na ga sun yi murmushi, nan take sai Indo ta kwala kira, nan da nan sai ga wata yarinya da ba ta wuce shekara 13 da haihuwa ba ta zo a guje, ta durkusa ta gaishe mu, sa’annan Indo ta ce ga wadda za ta rubuta mana nan, ’yar autata ce. Da wannan sana’a da muke yi na sa ta makarantar kudi domin ta samu ilimin zamani, baya ga na addini da take yi kullum, kuma alhamdulillah bukata ta fara biya, domin kuwa ko tsararrakinta da ke cikin birni, sun shafa mata lafiya. Wannan abu ya burge da sa mu cikin sabon tunani, ganin cewa tun ba mu shiga cikin rayuwar tasu ba, sun gano bakin zaren.

Minti kamar 30 muka yi muna hira da ’yar autar yarinyar cikin Ingilishi, nan muka fahimci cewa bisa ga dukkan alamu, sun shirya sanya wa ’yar auta tufafin da suka dace da ita a rayuwa.

Malam, bayan kamar kwana biyar da komawa gida sai ga sakon nasu ya zo, cikin kakkarwa na bude na fara karantawa, kuma rubutun tsaf, babu kura-kurai masu yawa. Ga abin da suke cewa:

“ Mun gode da kulawarku da kuma nuna damuwa game da halayen da muke ciki tattare da sauran ’yan uwa irinmu da ba ku samu ganawa da su ba, amma ku sani dukkan zantuttukan da muka yi da ku, sun kai kunnen saura, wannan bayani kuma da za mu yi muku da amincewar kowannenmu ne. Allah Ya biya.

Ku sani rayuwa mu a wurinmu ba ta wuce safara ba, ba mu san wani abu da za mu fada ba da ya wuce kaico da rashin makama. Yawancinmu kamar yadda kuka sani ba mu yi karatun boko ba, na Muhammadiyar ma ba mu yi nisa ba, ba kuma don babu tsarin bokon ko karatun allon a tattare da mu ba, sai dai don rashin sukunin da za mu iya samu mu yi wani abu daban da wanda muke yi a gidajen mazanmu.

Aure gare mu tamkar ba aure ba ne, domin cakude yake da hayagagar neman na rufin asiri. Kusan dukkanmu jirgi guda ya dauko mu. Tun muna kanana aka aurar da mu ga mazan da su kansu iyaye ke ciyar da su a gidajen gandu, su kansu iyayen nasu ba wata wadata suke da ita ba, balle mu sa ran samun sa’ida. Saboda haka rayuwar sai ta kasance mai tauri ga kowa da kowa. Haka muka tashi, muka girma cikin bidar abin rufin asiri, ba wai namu kadai ba, har da na mazan namu da kuma surukai.

Za mu ci gaba