✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nasiha zuwa ga maza (9)

Aure gare mu tamkar ba aure ba ne, domin cakude yake da hayagagar neman na rufin asiri. Kusan dukkanmu jirgi guda ya dauko mu. Tun…

Aure gare mu tamkar ba aure ba ne, domin cakude yake da hayagagar neman na rufin asiri. Kusan dukkanmu jirgi guda ya dauko mu. Tun muna kanana aka aurar da mu ga mazan da su kansu iyaye ke ciyar da su a gidajen gandu, su kansu iyayen nasu ba wata wadata suke da ita ba, balle mu sa ran samun sa’ida. Saboda haka rayuwar sai ta kasance mai tsauri ga kowa da kowa. Haka muka tashi, muka girma cikin bidar abin rufin asiri, ba wai namu kadai ba, har da na mazan namu da kuma surukai.

Kila ki ce ta yaya hakan ya kasance gare mu alhali muna da igiyar aure a rataye da mu? Bari in yi miki gwari-gwari domin mu fahimci juna. Akwai a cikinmu yarinya Iyami wadda ke auren Malam Kallamu Mai Almajirai, kullum kukanta bai wuce yadda za su kai magariba ba a cikin gidansu. Ba wai ana maganar almajirai ba ne kurum, ga ta tana da nata ’ya’yan da take fafutikar neman ciyar da su, ga kuma tarin almajirai da aka kawo wa Malam, wadanda ba su san yadda za su ciyar da tufatar da su ba, saboda haka ita da Malam da nata ’ya’yan duk sun rataya ne daga barar da almajiran ke yi a kullum rana domin a samu abin rufin asiri. Duk ranar da almajirai ba su samo ba ko kuma ba su ci sa’ar fita ba, to gidan da iyalan da ke ciki su kuma wannan rana sun shiga tasku. Ba kuma wani abu ya sanya Iyami shiga cikin wannan damuwa ba, sai don ba ta sanye da wata riga ta a -zo-a-gani, ga kuma girma an dora mata da ba ta san yadda za ta yi da shi ba. Nata ’ya’yan mata su ma sun bi nata tafarki tun suna kanana, ta yadda ba su san komai ba, in ba dogara ga almajirai ba, wannan ita ce rayuwar a kullum, ba kuma wani abu da za mu iya yi mata a matsayin kungiya don taimakawa.

Ki sani ba Iyami kadai ke cikin irin wannan hali ko yanayi ba. Haka Fauziyya ta kasance da nata mijin Mansur Sodangi. kullum rana ta Allah yana bisa titi neman kwadagon da zai ciyar da ita da kishiyarta da ’ya’yansu bakwai. A kullum ta zo wajen taro ba abin da take fada mana sai takaicin da suke fama da shi na rashin sanin makamar rayuwa. A kullum Mansur ya dawo gida ba abin da za su sarrafa domin ciyar da iyali, magana daya ce ya iya “ki yi ’yar dabarar nan taku ta mata mana,” ma’ana su san yadda za su yi su ciyar da kansu da tarin iyalin nasu da kuma shi maigidan nasu da ke can barga yana jiran agaji daga gare su. A kullum Fauziyya ta zo wajen taro kukanta daya ne, ba ta komai sai “’yar dabarar nan taku ta mata,”  da ta hada tura manyan ’ya’ya mata talla ko bakin kasuwa ko tasha ko ga-ludaya cikin gari domin su samo musu abin da za su ciyar da gidan da maigidan nasu, kullum kuma cikin ’yan dabarorin nasu suke, ita da abokiyar zamanta domin ganin ba su ji kunya ba. Ba kuma tana ganin laifin maigidan nasu ba ne da ya kasa, domin shi ma yana da nasa matsalolin, sai dai laifin nata ne da ita da ’yar uwarta da ba su samu tudun dafawa tun farkon gina rayuwar tasu a gidan miji ba. Shi ya sa talla da suke dora wa nasu ’ya’yan, musamman mata ta zama gata a wajensu, duk da sun san ba ita ce mafita ba.

Haka batun yake wajen su Tabawa Maituwo da kawayenta da ke zaune a bakin kasuwa suna yin sana’ar da za su rufa wa kansu asiri da kuma iyalansu. A kullum muka kira taro a unguwa ko gari domin tattauna matsalolinmu da ta iyalinmu ba su samun damar halarta, sai dai aiko sakon neman afuwa, kamar yadda suke cewa ba su da sukunin da za su leka wajen taron saboda awa 24 suke aikin sana’o’insu na sayar da tuwo ko waina ko dan wake da shinkafa ko koko da kosai da fura ko gasa masara ko dafawa ko soya gyada ko alale ko sayar da rake ko gwaiba ko makamantan haka. A kullum su Tabawa carar zakara suke jira ba wai kiran Sallah ba domin su fita filin daga, daga wadannan sana’o’in ne suke ci da sha da tufafar da iyali, ciki kuwa har da mazansu. Abin takaici shi ne sana’o’in nasu hannu-baka-hannu-kwarya ne, tamkar farar da ta isa gun itaciyar tumfafiya ce, nan gani, nan bari! Shi ya sa rani da damina suke cikin fasali guda na rayuwa, domin yawancin mazansu ba su da wani banki da ya wuce wadannan sana’o’in na matansu, nan cinsu yake, nan cin ’ya’yansu yake, nan ma kudaden karin mata da za su yi yake. Jiya ba ta canja ba, balle yau, ita kuwa gobe sai yadda ta kasance!

Ki sani, su Tabawa, ina ga ba wadanda suka kai su bauta a rayuwarmu ta yau da kullum, sanyin safiya ko ruwan sama, komai takin rana ba su hana su aiwatar da sana’o’insu na yau da kullum. Sa’annan ba lokacin tashi daga bakin sana’ar sai an samu abin da zai rufa asiri, ba kuma wani abu ya jawo musu wannan matsayi ba, ni a tawa fahimtar, sai don ba wata riga tattare da su sai ta ciyar da kai da iyali ko kuma wani ilimin da za a yi tokabo da shi a rayuwa. Tuwon nan ko kokon nan ko kuma dai kowace irin sana’a su ne mazansu ba mazan aure ba, domin su ne ruhin rayuwar. Haka suke gudanar da rayuwar da ta ’ya’yansu da sauran tarin al’ummar da ke tare da su a kullum.

Saboda haka idan har kika ce kuna neman wadanda za ku taimaka mawa ne daga cikin masu rauni a cikinmu, sai in ce masu raunin ai ba mu ne ba, sai dai mazanmu domin kuwa mu ne ginshikan da ke rike da gidajen da muke zaune, kila ma dukkan al’ummar da ke tattare da mu. Su wa ke neman taimako ke nan?

Za mu ci gaba