Categories: Kai-tsaye

Na’urar zabe sun ki aiki a tashoshi 49 na mazabun Sabon Gida, Gassol a Taraba

Sanadiyyar rashin aikin na’urar tantancewa ta sa masu kada kuri’a wadanda suka fito tun safiyar yau, basu sami damar kada kuri’a ba, sun nuna damuwarsu kan wannan lamari.

Wata majiya to shaidawa wakilin mu cewa ita na’urar zaben da aka tura yankin dama an shirya mata yin zabe a ranar 13 na wannan watan amma duk da dage zaben da aka yi a makon jiya ba a sauyawa na’urar ranar zaben  na yau ba.

ADVERTISEMENT

Wani mazaunin garin mai suna Yakubu Sabon gida, ya ce shi bai sami damar kada kuri’ar ba, sannan akwai runfunan zabe 49 a yankin akwai akalla masu kada kuri’a dubu 23 a yankin a mazabun Sabon gida kuma da gangan hukumar zabe ta sa na`urar zabe marasa kyau don a hana su yin zabe.

Jami`in wayar da kai na hukumar zabe ta Jihar Taraba mai suna Fabian Vwamhi ya ce, zai binciki lamarin sannan ya kira wakilinmu don yin bayani amma har yanzu bai kira ba.

ADVERTISEMENT
Jamilu Adamu

Recent Posts

Kirkiro Masarautun Kano: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci

Babbar kotun jihar Kano ta tsayar da ranar 14 ga Nuwamba 2019, a matsayin ranar da za a yanke hukunci…

1 hour ago

An yi arangama tsakanin ‘yan Kwankwasiyya da Gandujiyya a Kano

Akalla mutum takwas ne suka samu raunuka yayin da aka lalata motoci 10 a yau Litinin lokacin da aka yi…

2 hours ago

Kotu ta daure direba kan zargin yi wa agolarsa ciki a Abuja

Wata Kotun lardi ta birnin tarayya da ke Garin Jiwa Abuja, ta bada umarnin tsare wani direba mai shekara 36…

5 hours ago

’Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka 16 sun kashe ’yan banga 3 a Kaduna

Al'ummar Karamar hukumar Igabi da ke a jihar Kaduna sun waye gari cikin tashin hankali inda wasu ’yan bindiga suka…

5 hours ago

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi. Babban alkalin jihar Nasir Ajanah,…

11 hours ago

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda…

12 hours ago