Search
Subscribe
Nazari da tambihin kalaman kyautata rayuwa (1)

Nazari da tambihin kalaman kyautata rayuwa (1)

Muna kara godiya ga Allah (SWT) da a cikin ikonSa Ya ara mana lokaci da koshin lafiyar da muke ganawa da juna cikin wannan muhimmin fili na Sinadarin Rayuwa. Ina yi muku sallama mafi dacewa da kamalar dan Adam, assalamu alaikum. Bayan haka, yau kuma za mu tsunduma ne cikin bayyana da fassara wasu muhimman kalaman magabata, masu hikima, domin kuwa irin wadannan dunkulallun bayanai, fasihan malamai ne suka furta su, wadanda kuma suke kunshe da hikimomin kyautata rayuwarmu ta yau da kullum. Wasu kalaman ma, idan muka bi darussansu, za su amfane mu ba a nan duniya kadai ba, har ma da rayuwar gobe, kiyama.

Bari mu tafi kai tsaye wajen kawo wadannan kalamai da bayani. Wani mai hikima ya ce: “Jahili a tsakanin masu ilimi biyu, kamar bera ne a tsakanin kyanwoyi biyu.” Lallai kam, mu duba sosai mu ga tubalan da suka tada kunshiyar wannan bayani na hikima.

Mu dauki tubali na farko, wato ‘jahili.’ Idan muka lura sosai, jahili a rayuwarmu ta yau da kullum ya bani ya lalace, domin kuwa bai san komai ba kuma bai iya hassala komai na amfani a rayuwarsa. Ke nan ya zama koma baya, titibiri masomin gardi.

Tubali na biyu da ya bayyana a wannan kalami na sama shi ne ‘masu ilimi.’ A nan, za mu iya fahimta da cewa ilimi wani irin haske ne da ke tattare da alheri a kowane bangare. Mai ilimi kuwa, wani mutum ne da Allah Ya ba baiwar ni’ima ta wadata kowace iri, ya Allah wadatar zuci ko ta dukiya. Mai ilimi, mutum ne da zai iya sarrafa al’amura domin biyan bukatar kansa da rayuwarsa, idan ta yi yoyo ma, amfanin har ya game da sauran al’umma na kusa da shi da na nesa.

Sai mu dauki tubali na gaba, wato ‘bera.’ A nan, kowa dai ya san abin da ake kira bera, wanda wata karama kuma fitinanniyar halitta ce da ta yi kaurin suna a tsakanin bil-Adama. Kowa ya san bera wajen wuce-gona-da-iri, kowa ya san shi da ha’inci da sata da binciken abin da bai ajiye ba kuma bai ba kowa ajiya ba. A takaice, kowa ya tsani bera, domin kuwa halitta ce da ke haifar da rashin sukuni a cikin al’umma. Dalili ke nan ya sanya, duk inda bera yake zaune, za ka ga ana farautarsa, ana kashewa.

Sai kuma tubali na gaba kuma na karshe da ya bayyana a cikin wannan kalamin hikima na sama, watau ‘kyanwoyi biyu.’ Ita kyanwa, ba kamar bera ba, ita halitta ce mai daraja da kima a idon al’umma. Tana da wata karama ta musamman, wacce ta haka ta zama abin kauna kuma abin sha’awa ga mutane. Haka kuma, ta mallaki wata mu’ijiza da ke yin barazana da tsoratarwa ga bera.

Kasancewar mun warware jigogi ko tubalan da suka harhada kunshiyar sakon da ke cikin wannan kalamai na hikima, za mu gane cewa lallai akwai darasin da zai amfani rayuwarmu a cikinsa. Domin kuwa, a lokacin da jahili ya zama cikin kuncin rayuwa da takura, shi kuwa mai ilimi zai kasance cikin wadata da muhibba a rayuwa. Kamar dai yadda bera (jahili, marar karfi) zai kasance a tsakanin kyanwoyi (masu hikima, ilimi da karfi).

Babban darasin da za mu iya tsinta daga wannan bayani shi ne, muhimmancin ilimi da kuma rashin muhimmancin jahilci. Dan uwa, ’yar uwa, wane kuka zaba? Na tabbata kowa zai so ya kasance cikin jin dadin rayuwa, cikin muhibba da daukaka. Na tabbata babu mai son ya kasance wulakantacce, marar arziki, kuma mai rayuwar kunci. Idan haka ne, sai mu tashi tsaye mu nemi ilimi kasa rika, wanda haka zai sanya idan mun same shi za mu zama masu ilimi, wanda haka zai sanya mu kauce wa tudun jahilci. Domin kuwa duk wanda ya zabi ya zama jahili, to ya bani ya lalace a rayuwarsa.

Za mu ci gaba

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin