Search
Subscribe
Nazari da tambihin kalaman kyautata rayuwa (2)

Nazari da tambihin kalaman kyautata rayuwa (2)

Tare da gaisuwar mutunci, assalamu alaikum, ya ku masu karanta wannan muhimmin fili na Sinadarin Rayuwa! Yau  za mu ci gaba da kashi na biyu na fashin bakin wasu kalaman da za su kyautata mana rayuwa. Kamar yadda na fada a makon jiya, na ce irin wadannan kalamai da muke bayaninsu, muna tsintsinto su ne daga wurare daban-daban, kuma mutane masu hikima da fasahar magana ne suka furta su a lokuta da zamunna daban-daban. Wasu bayanan ma an same su ne kacokan daga babban littafi (Alkur’ani) ko kuma Hadisan Manzon Allah (SAW). Da ma Manzon Tsira, ya shaida mana cewa hikima kayan mumini ne, duk inda ya iske ta, sai ya dauki abarsa kawai. Bisa la’akari da wadannan bayanai, ya dace mu zizara wa rayuwarmu Sinadarin Rayuwa, musamman ta kasancewa masu neman ilimi, domin kasancewa masu ilimi ba jahilai ba, sannan mu kasance masu aiki tukuru ba shagwababbu ba.

A makon jiya mun kammala wani bayanin, ga wani kuma, inda shi ma wani mai hikima da balagar harshe ya ce: “Wahala, ita ke haifar da kwazo, a yayin da shagwaba ke kashe kwazo.”

Masu hikimar Hausa ma na cewa, dole uwar na ki, a yayin da suka kara da cewa, wahala ko wuya ba ta kisa. Idan muka nazarci wannan bayanin hikima da ya gabata a sama, za mu fahimci tsagwaron sakon da ke cikinsa. A takaice, yana kira ne ga mutane su mike su yi aiki tukuru, domin neman na kai. Idan mutum ya tashi tsaye, ya yi aiki kamar da azazza, ba tare da jin nauyin jiki ko kasala ba, babu shakka zai kasance mai kwazo; wannan kwazo kuwa zai haifar masa da nasara a rayuwa. Dalili ke nan ma masu hikimar tarbiyyar yara suka ce, ka ki naka, duniya ta so shi, ka so naka, duniya ta ki shi.

A lokacin da wahala ta haifar da kwazo ga mutum, ita kuma shagwaba, za ta lalata wa mutum kwazo ne. Duk mutumin da ya tashi cikin laushi da shagwaba, ya tashi a matsayin dan lele, wanda komai sai dai a yi masa, bai san ya motsa jiki domin neman abin zaman duniya ba, babu shakka ba zai gane muhimmancin nema ba. Domin kuwa bai san zafin nema ba. Idan haka ta kasance, mutum zai zama koma-baya ta fuskar rayuwa, zai zama malalaci, wanda ba zai iya samun wata nasara ba a rayuwarsa.

Duk da cewa Hausawa sun ce, zafin nema ba ya kawo samu, to kuma zaman laushi ba zai iya haifar da komai ba sai daskarewa da mutuwar zuciya. Mutumin da ke son samun nasarar rayuwa, shi ne mai buri, mai kokarin neman cikar burinsa ta hanyar jajircewa da kokari ga duk abi da ya sanya a gaba.

Bari mu ji wannan kalamin, wanda wani masani ya fada, inda yake cewa: “Baki kamar kifi suke, bayan kwana uku sun fara doyi.” Kamar yadda za mu gani, wannan kalami na dauke da tubala kamar uku da ke dauke da ma’anoninsa. Bari mu dauki tubalan daya bayan daya, domin mu fasa bakin ma’anar gundarin kalaman.

Tubali na farko da ya gina wannan bayani, shi ne kalmar ‘baki.’ Baki na nufin wadansu mutane da suka sauka a wani wuri da ba mazauninsu ba na ainihi. Wato sun bar wurarensu na zama, sun je wani wurin na daban, ya alla ko don ziyara ko wani dalili na daban. Ke nan ba nan za su ci gaba da zama ba, komai dadewa, za su koma gidajensu na ainihi.

Tubali na biyu da ya gina kalaman da muka dauko, shi ne kalmar ‘kifi.’ Kifi dai kamar yadda muka sani, wata halitta ce mai rayuwa a cikin ruwa. Jikin kifi na da santsi sosai, kuma da zarar an raba shi da ruwa, to ba zai iya rayuwa mai dadewa ba, zai mutu. Idan ya mutu kuwa, to idan ba cikin kankara aka adana shi ba, babu shakka zai yi wari, akalla bayan kwana uku.

Za mu ci gaba

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin