Da Dumi Dumi

Nazari da tambihin kalaman kyautata rayuwa (5)

Kamar yadda muka faro fashin bakin wasu zababbun kalaman hikima na kyautata rayuwarmu, yau ma dai za mu ci gaba, amma kafin sannan, bari mu yi musabahar da muka saba a kullum; Assalamu alaikum.

Bari mu fara da wani kalamin hikimar, wanda shi ma wani fasihin, wanda ba mu tantance shi ba ne ya furta shi, abin da yake cewa shi ne: “Idan kowa ya zama gwani, to wa zai nuna murnar gwanintar?” Wannan kalami na nuna mana cewa, halaye dai da yanayin mutane sun bambanta da na juna. Wato dai ba duka aka taru aka zama daya ba. Idan wane gwanin tuki ne, to wane kuma gwanin saka ne ko gwanin jima. Abin da wani ya kware, wani kuwa bai kware a kansa ba. Ta haka za a samu mabambantan mutane da suka gwanance kuma suka shahara a fagage daban-daban. Idan haka ta faru, sai wannan ya yaba wa wancan, shi ma wancan ya yaba da wancan. Ta haka za a samu kokari da kara himma daga rukunan jama’a daban-daban. Wannan yanayin zai haifar da ci gaba a dukkan al’amuran jama’a. Amma idan kowa ya zama gwani, shi ke nan, babu wanda zai burge wani, babu wanda zai tada wani idan wani ya fadi. Ke nan abin kirki ne ga al’umma a kasance daban-daban ta fannoni da dama. Wanan shi ke haifar da ci gaba cikin al’amuran jama’a. Da zarar wani ya yi gwaninta, sai a samu wadanda za su yi murna da mamaki da yabawa; haka zai sanya gwanin ya kasance cikin murna da farin ciki. Wannan zai sanya shi ma wancan ya yi kwadayin zama gwani a fagensa. Sakamakon da za a samu cikin mutane sai ya zama mai amfani kuma mai yawa.

Darussanmu na yau sun kasance har guda uku, na farko shi ne, mu zama masu dagewa, jajircewa da nacewa wajen fuskantar ayyukanmu da harkokinmu na rayuwa, wanda ta haka ne za mu samu gamsasshiyar nasara. Sai kuma mu kula da maganganun da muke furtawa, domin mu kasance masu kamala ba wawaye ba. Darasi na uku kuma shi ne, mu gane fa’ida da muhimmancin bambance-bambancen da ke tsakaninmu. Allah Ya sanya mu dace, amin.

Ga kuma wani muhimmin kalami da wani magabaci da ban tantance sunansa ba ya fada, inda yake cewa: “Kada ka bari sai gobe, abin da za ka iya yi a yau.” Wannan batu yana da tsananin muhimmanci da tasiri a rayuwarmu, musamman idan muka nazarce shi da idon basira. Kamar yadda za mu gani, abu na farko da za mu iya tsinkaya daga batun nan shi ne, muhimmancin lokaci a rayuwa. Za mu iya gane haka idan muka dan yi nazari kan muhimman tubalan lokaci guda uku, wato jiya da yau da kuma gobe. Cikin wadannan tubala ne za mu iya fahimtar wannan muhimmin batu.

Idan muka nazarci jiya, za mu fahimci cewa ta riga ta wuce, kuma ba za ta dawo ba har abada. Duk abin da mutum ya aikata a cikinta, ya riga ya shude, idan na kirki ne, mutum ya ci riba ke nan. Idan kuma ba na kirki ba ne, to ya ci baya ke nan. Idan ma mutum bai aikata komai ba a cikin jiya din nan, wannan ya nuna cewa mutum ya yi asarar jiya din nan ke nan, domin kamar yadda muka ambata, ta wuce, ba za ta yo ribas ta dawo ba domin ka aikata abin da kake son aikatawa. Amma duk da haka, muhimmancin jiya din nan shi ne, mutum zai samu damar nazarinta, sannan ya gano abin da ya aikata a cikinta. Idan wani abin kokari ya yi, zai yi farin ciki, sannan ya kara kokari a yau domin ganin cewa ya ninka aikata irinsa a yau. Idan kuma ba mai kirki ba ne, sai mutum ya yi nadama a yau, sannan ya kudiri aniyar hana kansa aikata irinsa a yau. Haka dai batun yake idan mutum ya zama bai aikata komai ba a jiya, sai ya himmatu domin ganin ya aikata wani abu mai muhimmanci a yau da Allah Ya nuna masa.

ADVERTISEMENT

Za mu ci gaba

Share