Da Dumi Dumi

Nazari da tambihin kalaman kyautata rayuwa (6)

Kamar yadda muka faro fashin bakin wasu zababbun kalaman hikima na kyautata rayuwarmu, yau ma dai za mu ci gaba, amma kafin sannan, bari mu yi musabahar da muka saba a kullum; Assalamu alaikum.

Ita kuwa yau, wacce ita muke ciki, tsananin muhimmancinta yana da yawa, musamman ma ganin cewa wata dama ce da muka sake samu, wacce ta bambanta da jiya. Tsagwaron darasin wannan kalami namu na sama, yana kunshe ne a cikin ita yau din. Don haka sai mutum ya yunkura, ya aikata abin kirki a cikin yau din. Zai yi haka ne ta kwatanta abubuwan da ya yi a jiya, domin sake kwatanta su ko kuma ma ya ninka su, musamman idan masu muhimmanci ne. Yau za ta ba mutum damar kauce wa fadawa cikin irin kuskuren da ya aikata a jiya, sannan idan ma ya zama bai aikata komai ba a jiyan, sai ya yunkura, cikin himma domin ganin cewa ya aikata wani abu na amfani a rayuwarsa.

A nan, ya kamata mu sake nazarin batun nan dai namu na sama, cewa duk abin da ka san za ka iya aikatawa a yau, ko a yanzu, to ka aikata shi kawai gaba gadi, kada ka ce bari in bari sai anjima ko kuma sai gobe. Wannan hukunci da ka yanke yana da hadari sosai, domin kuwa a yau ne kuma a yanzu ne kake da iko da damar yin wani abu, domin ba ka san yadda za ta kasance anjima din ko goben ba. Idan kuwa ka aikata wani abu yanzu-yanzu, to ka karu ke nan, kuma ka rage wa kanka wata wahala, wacce idan ka bari cewa sai gobe ko sai anjima, idan har Allah Ya kai mu an jima din ko goben, to tana iya zuwa da irin nata matsalolin da bukatun, wadanda suka sha bamban da na dazu ko na jiya din. Ke nan, ka samu aiki biyu ko uku ke a lokaci guda, maimakon daya, domin na dazu ko na jiya na nan ba ka aikata ba, sannan ga kuma wani na yanzu da ya kawo kansa, wanda kuma ya zama dole sai ka aikata shi. Domin kauce wa haka, sai ka mike kawai, yanzu-yanzu, ba sai an jima ba, ka aikata abin da za ka iya aikatawa.

Idan muka duba tubali na uku kuma, wato gobe, za mu fahimci cewa ba ta zo ba tukunna, kuma ba mu da tabbacin zuwanta, amma duk da haka ba shantake kafa za mu yi mu sanya idon zuwan nata ba kawai. A’a, za mu yi wani dan kokari ne irin daidai namu, domin kuwa a matsayinmu na mutane, muna da bukatu da burace-burace da muke da nufin aikatawa idan mun samu dama. Ga shi kuma mun aikata wani abu jiya, ba mu gama ba, muka ci gaba da shi yau, ba mu kammala ba, sai mu jefa shi cewa, idan Allah Ya nuna mana gobe lafiya, za mu ci gaba. Wannan buri na cewa gobe, in Allah Ya kai mu zan ci gaba da kaza, shi ne abin bukata, shi ne tsarin da za ka sanya a zuciyarka, kuma kada ka sake ya kauce daga kwakwalwarka; idan da hali ma, dauki alkalami ka rubuta shi, domin kada ka mance.

Da zarar Allah Ya nuna maka gobe din nan, ka ga kana da burinka, kuma ka yi nazarin hanyoyin da za ka bi domin cin ma aiwatar da shi. Idan Allah Ya ba ka iko da damar aiwatarwa, ka ci gajiya da ribar wannan lokaci ke nan. Har kullum ita rayuwarmu, ba tabbas ke gare ta ba, don haka a matsayinka na mutum, sai ka yi iyaka kokarinka daidai ikonka. Babban abin da dai ba a so shi ne zaman dirshan, watau zaman kashe wando. Wannan babbar cuta ce, babbar illa ce da ke dakushe ci gaban mutum da al’umma baki daya.

ADVERTISEMENT

Idan muka duba darasinmu na yau, za mu fahimci babbar fa’idar lokaci, sannan kuma mu gane cewa kasala halayya ce marar amfani ga dan Adam. Wadannan abubuwa biyu, su za mu tantance domin fa’idantar da rayuwarmu ta yau da kullum. Shi dai lokaci, mu yi amfani da shi a yau, a yanzu, ba sai anjima ko sai gobe ba. Ita kuwa ganda da kasala da kyuya, duk mu kauce mata, mu yake ta, domin abokiyar gaba ce, wacce ke hana mana ci gaba a rayuwa.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya