Da Dumi Dumi

Nazari da tambihin kalaman kyautata rayuwa (8)

Idan muka duba lungu da sako na rayuwarmu ta yau da kullum, ana samun shugabanni da shugabanci a ko’ina, kuma a sakade-sakade na rayuwarmu ta yau da kullum. Akwai shugabanci babba akwai kuma matsakaici da kuma karami. Misali, a can kololuwar tsanin shugabanci, ana samun Shugaban Kasa, ga Gwamna ga Shugaban Karamar Hukuma. A yanki ko unguwa kuwa, akwai kansila. Idan muka sauko kasa kuwa, wato muka shiga cikin gidan iyali, akwai uba, akwai uwa, akwai wa ko ya da sauransu. Wadannan duk misalai ne na shugabanni. Idan muka sake duba wani sashin kuma, a ma’aikatu da wurin sana’o’i, duk wanda ke saman wani ko wasu da ke aiki ko sana’a a karkashin mutum, to ya zama ko ta zama shugaba.

Idan mun gamsu ko mun fahimci wadannan misalai na shugabanni, to wannan kalami na mai hikima na sama da su yake kai-tsaye. Kada Shugaban Kasa ya ba da umarnin cewa a yi kaza, alhali ba zai jajirce ya tsaya kai da fata domin ganin ya zartar ko ya gudanar da wannan umarni ba. Haka shi ma Gwamna a jiharsa, ko shugaban karamar hukuma a yankinsa, ko kuma kansila a unguwarsa. Haka shi ma maigida a gidansa, kada ya ba da umarnin wani hukunci cikin gidansa a yau, an jima kuma ya warware shi ba tare da wani dalili ba, ko kuwa ya yi sako-sako wajen zartar da shi.

Ko mun gane fa’idar duk wannan misali da kwatance? Idan ma ba mu gane ba, bari mu yi dalla-dalla. Idan shugaba ya kasance mai ba da ummurnin cewa a yi wani abu, amma bai tsaya kan hanyar da zai tabbatar an bi umarnin ba, wato ya kasa zartar da umarnin da ya bayar, to ya haifar da babbar baraka ke nan a ma’aikatarsa ko a gidansa. Domin kuwa al’amura ba za su rika gudana cikin fa’ida ba, ba za a rika samun nasarar tafiyar da al’amuran yau da kullum cikin nasara da fa’ida ba. Misali, sai maigida ya ce wa yaransa, a kullum za mu rika zuwa gona. Me ya kamata ya yi domin ganin cewa wannan umarni da ya bayar ga yaransa ya samu nasara? Babban abin da zai yi shi ne, tun ma kafin ya bayar da wannan umarni, ya tabbatar da cewa ya shirya wa tafiya gonar nan, ya tanadar da dukkan muhimman abubuwan da za su taimaka musu domin tafiya gonar nan. Wadannan kuwa sun hada da kayan aiki da kuma samar da yanayin da zai saukaka musu tafiya gonar nan. Haka kuma domin a samu gamsasshiyar nasara, mai gidan nan sai ya shiga gaba, ya jagoranci yaransa zuwa gonar nan. Idan an je gonar kuma, ba umarni kadai zai tsaya bayarwa ba, sai ya yi aikin tare da yaran nasa a aikace, sannan ya share musu hanyar da za su bi su gane yadda yake son a aiwatar masa da aikin.

Haka kuma, shugaba, kowane iri ne, yana bukatar ya tabbatar da cewa duk wani kudiri nasa, mai aiwatuwa ne, kudiri ne da ya dace da yanayin da za a iya gudanar da shi cikin fa’ida. Wannan zai sanya idan ya ce ga abu kaza da yake son aiwatarwa ko kuma a aiwatar masa, to abin zai yiwu, sannan kuma ya tabbatar ya tanadar da kayayyaki ko abubuwan da za su tabbatar da yiwuwar wannan kuduri.

Maigida a cikin iyalinsa, shi ma haka zai yi domin gudanar da tafiyar mulkin gidansa. Ya tabbatar ya tsaya da kafafunsa wajen zartar da duk wani kuduri da ya furta, kuma ya nemi a aiwatar a gidansa.

ADVERTISEMENT

A takaice, darasin da za mu iya dauka daga maudu’inmu na yau shi ne, duk abin da mutum zai yi, ya shirya masa sannan ya yi kokarin tsayawa domin tabbatuwarsa. Kada a samu mutum yana yin alkawarin karya, ko kuma ya rika jajibe-jajiben abuwan da ya tabbata sun fi karfinsa, sun fi karfin aiwatarwar na kasansa. Gargadin dai shi ne, kada ka ba da umarnin hukuncin da ka san ba za ka iya zartarwa ba.

Mun kammala

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya