✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nazarin kalaman azanci domin kyautata rayuwa (04)

Tare da gaisuwar mutunci, Assalamu alaikum. Ya ku masu karanta wannan muhimmin fili na Sinadarin Rayuwa, yau kuma za mu ci gaba da kashi na…

Tare da gaisuwar mutunci, Assalamu alaikum. Ya ku masu karanta wannan muhimmin fili na Sinadarin Rayuwa, yau kuma za mu ci gaba da kashi na uku na nazarin wasu kalaman da za su kyautata mana rayuwa. Kamar yadda na fada a makon jiya, na ce irin wadannan kalamai da muke bayaninsu, muna tsintsinto su ne daga wurare daban-daban kuma mutane masu hikima da fasahar magana ne suka furta su a lokuta da zamunna daban-daban. Wasu bayanan ma an same su ne kacokan daga babban littafi (Alkur’ani) ko kuma hadisan Manzon Allah (SAW). Da ma manzon na tsira, ya shaida mana cewa ilimi kayan mumini ne, duk inda ya iske shi, sai ya dauki abinsa kawai.
Bari mu fara da wannan kalamin, wanda wani masani ya fada, inda yake cewa: “Baki kamar kifi suke, bayan kwana uku sun fara doyi.”
Kamar yadda za mu gani, wannan kalami na dauke da tubala kamar uku da ke dauke da ma’anoninsa. Bari mu dauki tubalan daya bayan daya, domin mu fasa bakin ma’anar gundarin kalaman.
Tubali na farko da ya gina wannan bayani, shi ne kalmar ‘baki.’ Baki na nufin wasu mutane da suka sauka a wani wuri da ba mazauninsu ba na ainahi. Watau sun bar wurarensu na zama, sun je wani wurin na daban, ya Allah ko don ziyara ko kuma wani dalili na daban. Ke nan ba nan za su ci gaba da zama ba, komai dadewa, za su koma gidajensu na ainahi.
Tubali na biyu da ya gina kalaman da muka dauko, shi ne kalmar ‘kifi.’ Kifi dai kamar yadda muka sani, wata halitta ce mai rayuwa a cikin ruwa. Jikin kifi na da santsi sosai, kuma da zarar an raba shi da ruwa, to ba zai iya rayuwa mai dadewa ba, zai mutu. Idan ya mutu kuwa, to idan ba cikin kankara aka adana shi ba, babu shakka zai yi wari, akalla bayan kwana uku.
Tubali na uku, kamar yadda za mu nazarta, shi ne kalmar ‘doyi.’ Shi doyi wani irin yanayi ne marar dadi da ke bayyana, wanda za a iya ji ta shaka a hanci. Daidai yake da wari, watau kishiyar kamshi ke nan.
Tun da mun yi fashi bakin tubalan da suka gina wannan bayani na hikima da muka nazarto, yanzu kuma za mu shiga ma’anar kalamin gaba daya. A nan, abin fahimta daga bayanin nan shi ne, iyaka hakuri da dawainiyar da za a yi da bako shi ne kwana uku. Da zarar ya wuce kwana uku, ya zama kunci da lalura ga mutane. Don haka, idan za ka yi bakunci, ka tabbatar kada ka wuce kwanaki uku, domin iyaka adadin lokacin da za ka samu farin cikin bakuncinka daga mai masaukinka ke nan. Idan kuwa ka zarce kwana uku, to babu shakka za ka ga canjin yanayi da canjin fuska daga mai masaukinka. Domin ita rayuwa, ’yar kula ce, dole sai mun kula da abin da zai je ya zo, domin kauce wa kuntata wa rayuwarmu da rayuwar abokan zumuncinmu.
Haka kuma, wannan na nufin cewa duk wani abu da za mu yi, mu nemi ilimi a kansa, mu kuma gane alfanunsa da tasirinsa. Da haka ne za mu iya aiwatar da rayuwarmu cikin fa’ida. Ta haka ne kuma za mu lizimci kiyayen hakkokin juna, yadda za a gudu tare kuma a tsira tare, ba tare da takura wa juna ba.
A nan, idan za ka tafi bakunta zuwa ga wasu, ya Allah wani gari ne ko wata kasa; sa ka yi nazari ka tambayi kanka, shin wace irin ziyara za ka kai? Shin ziyara ce ta zumunci da musabaha da juna ko kuwa ta neman ilimi ce? Ko kuwa za ka tafi da nufin zama ne na aiki ko na wani abu? Idan ka gano irin bakuncin da za ka yi, to lallai ne sai ka tanadi guzuri da abubuwan da za su taimaka maka, har iya zamanka. Idan ziyarar gaisuwa ce, wato zumunci ko makamanciyarta, to ka sani cewa kada ka wuce kwana uku, domin da ka gota wannan adadin, to ba za ka ji dadin bakuncinka ba. Allah sa mu dace, amin.
Za mu ci gaba