✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nazarin kalaman azanci domin kyautata rayuwa (07)

Muna kara godiya ga Allah (SWT) da a cikin ikonSa Ya ara mana lokaci da koshin lafiyar da muke saduwa da juna cikin wannan muhimmin…

Muna kara godiya ga Allah (SWT) da a cikin ikonSa Ya ara mana lokaci da koshin lafiyar da muke saduwa da juna cikin wannan muhimmin fili na Sinadarin Rayuwa. Ina yi maku sallama mafi dacewa da kamalar dan Adam, Assalamu alaikum.
Muna ci gaba da nazarin kalaman azanci domin kyautata rayuwa. Don haka bari mu duba wani kalamin hikima, wanda wani fasihin da ba mu tantance shi ba ya furta. Ga abin da yake cewa: “Idan kowa ya zama gwani, to wa zai nuna murnar gwanintar?”
A wannan kalami na azanci, akwai muhimman kalmomi da ya kamata mu mayar da hankali a kansu, wato kalmomin ‘gwani’ da ‘murna.’ Idan aka ce wane gwani ne, ana nufin ya kware kuma ya gwanance a harkar da yake yi. Misali, ana samun gwani a fagage daban-daban na rayuwa, kamar gwanin tukin mota ko jirgin sama ko gwanin likita da sauransu.
Kalmar murna kuwa na nufin nuna jin dadi ga faruwar wani abu. Ke nan idan wani ya nuna kwarewa ko gwaninta, za a samu mutane suna yi masa murna, suna yaba masa, wanda hakan zai kara masa kwarin gwiwa da jin dadi. Ta haka ne zai samu gamsuwa, sannan kuma ya sake samun karsashi. Hakan zai sanya ya kara azama domin ci gaba da aiwatar da wannan aiki da ya kware a kansa. A haka kuma al’umma za su ci gaba da amfana da ilimin nasa.
Wannan azancin kalami ke nan yana nuna mana cewa halaye dai da yanayin mutane sun bambanta da na juna. Watau dai ba duka aka taru aka zama daya ba. Idan wane gwanin tuki ne, to wane kuma gwanin saka ne ko gwanin jima. Abin da wani ya kware, wani kuwa bai kware kansa ba. Ta haka za a samu mabambantan mutane da suka gwanance kuma suka shahara a fagage daban-daban. Idan haka ta faru, sai wannan ya yaba wa wancan, shi ma wancan ya yaba da wancan. Ta haka za a samu kokari da kara himma daga rukunan jama’a daban-daban.
Wannan yanayin zai haifar da ci gaba a dukkan al’amuran jama’a. Amma idan kowa ya zama gwani, shi ke nan, babu wanda zai burge wani, babu wanda zai tada wani idan wani ya fadi. Ke nan abin kirki ne ga al’umma a kasance daban-daban ta fannoni da dama. Wannan shi ke haifar da ci gaba cikin al’amuran jama’a. Da zarar wani ya yi gwaninta, sai a samu wadanda za su yi murna da mamaki da yabawa; haka zai sanya gwanin ya kasance cikin murna da farin ciki. Wannan zai sanya shi ma wancan ya yi kwadayin zama gwani a fagensa. Sakamakon da za a samu cikin mutane sai ya zama mai amfani kuma mai yawa.
Darussanmu na yau sun kasance har guda uku, na farko shi ne, mu zama masu dagewa, jajircewa da nacewa wajen fuskantar ayyukanmu da harkokinmu na rayuwa, wanda ta haka ne za mu samu gamsassar nasara. Sai kuma mu kula da maganganun da muke furtawa, domin mu kasance masu kamala ba wawaye ba. Darasi na uku kuma shi ne, mu gane fa’ida da muhimmancin bambance-bambancen da ke cikinmu.