✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nazarin kalaman azanci domin kyautata rayuwa 12

Assalamu alaikum, ya ku ma’abuta karanta wannan mashahurin fili na Sinadarin Rayuwa. Bayan haka, yau mako na tara ke nan da muke nitso da ninkaya…

Assalamu alaikum, ya ku ma’abuta karanta wannan mashahurin fili na Sinadarin Rayuwa. Bayan haka, yau mako na tara ke nan da muke nitso da ninkaya cikin tambihi kan wasu fitattun kalamai da wasu magabata masu hikima da fasaha suka ambata, a lokuta mabambanta. A wannan makon ma, za mu nazarci wasu daga irin wadannan kalamai, da nufin samun daidaito da natsuwa a rayuwarmu. Babbar fa’idar dai ita ce, Allah Ya yi mana gamo da katar, wajen cin nasara a nan duniya da kuma babban gidan da muka nufa.
Da farko, bari mu fara nazarin kalamin wani mai hikima, wanda ya ce: “A rayuwa, kada ka ba da ummurnin hukuncin da ka san ba za ka iya zartarwa ba.”
Idan mun bi kadin wannan kalami, za mu tsinci tubala kamar guda uku, muhimmai da suka tada ma’anoni da hikimomin da ke cikinsa.
Tubali na farko shi ne ‘rayuwa.’ Ba sai an kai ruwa rana ba kuma ba tare da raba daya biyu ba, an san dai ma’anar rayuwa, watau yadda rayukanmu ke shudawa da wakana cikin zamanmu na duniya a yau da gobe. Tubali na biyu kuwa shi ne ‘ummurni.’ Ma’anar wannan kalma, kamar yadda ta fito a cikin gundarin kalaman hikima da muka ambato a sama shi ne, ana nufin mutum ya bukaci a aiwatar ko a zartar da wani abu, ya Allah na zahiri, idan na aiki ne ko kuma na bin wani sharadi. Tubali na uku kuwa shi ne ‘zartarwa.’ A takaice, zartarwa na nufin gudanarwa ko aikatawa ko tabbatarwa da sauransu.
Ko ta yaya za mu gano gundarin ma’anar da ke cikin wannan kalami? Abin da za mu yi ke nan, musamman domin mu fa’idantu da hikimomin da ke kunshe a cikinsa. A kai tsaye, wannan kalami na gargadi ne ko yin ishara ga duk wanda ya samu kansa bisa wani shugabanci da cewa ya tsaya tsam da ransa domin nazarin duk wani hukunci da zai ba da ga na kasa da shi domin gudanarwa ko zartarwa.
Idan muka duba lungu da sako na rayuwarmu ta yau da kullum, ana samun shugabanni da shugabanci a ko’ina, kuma a sakade-sakade na rayuwarmu ta yau da kullum. Akwai shugabanci babba akwai kuma matsakaici da kuma karami. Misali, a can kololuwar tsanin shugabanci, ana samun Shugaban kasa, ga Gwamna ga Shugaban karamar Hukuma. A yanki ko unguwa kuwa, akwai kansila. Idan muka sauko kasa kuwa, watau muka shiga cikin gidan iyali, akwai uba, akwai uwa, akwai wa ko ya da sauransu. Wadannan duk misalai ne na shugabanni. Idan muka sake duba wani sashin kuma, a ma’aikatu da wurin sana’o’i, duk wanda ke saman wani ko wasu da ke aiki ko sana’a a karkashin mutum, to ya zama ko ta zama shugaba.
Idan mun gamsu ko mun fahimta da wadannan misalai na shugabanni, to wannan kalami na mai hikima na sama da su yake kai tsaye. Kada Shugaban kasa ya ba da ummurnin cewa a yi kaza, alhali ba zai jajirce ya tsaya kai da fata domin ganin ya zartar ko ya gudanar da wannan ummurni ba. Haka shi ma Gwamna a jiharsa, ko Shugaban karamar Hukuma a yankinsa, ko kuma Kansila a unguwarsa. Haka shi ma maigida a gidansa, kada ya ba da ummurnin wani hukunci cikin gidansa a yau, anjima kuma ya warware shi ba tare da wani dalili ba, ko kuwa ya yi saku-saku wajen zartar da shi.
Ko mun gane fa’idar duk wannan misali da kwatance? Idan ma ba mu gane ba, bari mu yi dalla-dalla. Idan shugaba ya kasance mai ba da ummurnin cewa a yi wani abu, amma bai tsaya kan hanyar da zai tabbatar an bi ummurnin ba, watau ya kasa zartar da ummurni da ya bayar, to ya haifar da babbar baraka ke nan a ma’aikatarsa ko a gidansa. Domin kuwa al’amura ba za su rika gudana cikin fa’ida ba, ba za a rika samun nasarar tafiyar da al’amuran yau da kullum cikin nasara da fa’ida ba. Misali, sai maigida ya ce wa yaransa, a kullum za mu rika zuwa gona. Me ya kamata ya yi domin ganin cewa wannan ummurni da ya bayar ga yaransa ya samu nasara? Babban abin da zai yi shi ne, tun ma kafin ya bayar da wannan ummurni, ya tabbatar da cewa ya shirya wa tafiya gonar nan, ya tanadar da dukkan muhimman abubuwan da za su taimaka musu domin tafiya gonar nan. Wadannan kuwa sun hada da kayan aiki da kuma samar da yanayin da zai saukaka musu tafiya gonar nan. Haka kuma domin a samu gamsassar nasara, maigidan nan sai ya shiga gaba, ya jagoranci yaransa zuwa gonar nan. Idan an je gonar kuma, ba ummurni kadai zai tsaya bayarwa ba, sai ya yi aikin tare da yaran nasa a aikace, sannan ya share musu hanyar da za su bi su gane yadda yake son a aiwatar masa da aikin.
Haka kuma, shugaba, kowane iri ne, yana bukatar ya tabbatar da cewa duk wani kuduri nasa, mai aiwatuwa ne, kuduri ne da ya dace da yanayin da za a iya gudanar da shi cikin fa’ida. Wannan zai sanya idan ya ce ga abu kaza da yake son aiwatarwa ko kuma a aiwatar masa, to abin zai yiwu, sannan kuma ya tabbatar ya tanadar da kayyaki ko abubuwan da za su tabbatar da yiwuwar wannan kuduri.
Maigida a cikin iyalinsa, shi ma haka zai yi domin gudanar da tafiyar mulkin gidansa. Ya tabbatar ya tsaya da kafafunsa wajen zartar da duk wani kuduri da ya furta, kuma ya nemi a aiwatar a gidansa.
A takaice, darasin da za mu iya dauka daga maudu’inmu na yau shi ne, duk abin da mutum zai yi, ya shirya masa sannan ya yi kokarin tsayawa domin tabbatuwarsa. Kada a samu mutum yana yin alkawarin karya ko kuma ya rika jajibe-jajiben abubuwan da ya tabbata sun fi karfinsa, sun fi karfin aiwatarwar na kasansa. Gargadin dai shi ne, kada ka ba da ummurnin hukuncin da ka san ba za ka iya zartarwa ba.