Da Dumi Dumi

Naziru Sarkin Waka ya yi murabus daga sarautar

Bayan tube Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, Sarkin Wakar Sarkin Kano Alhaji Naziru M. Ahmad ya yi murabus daga sarautarsa.

Fitaccen mawakin wanda aka fi san da Sarkin Waka ya bayyana haka ne a wata wasika da Aminiya ta samu, inda ya ce, “Na rubuta wannan wasikar ce domin in bayyana muku cewa na yi murabus daga sarautar Sarkin Wakar San Kano daga ranar 13 ga Maris, 2020.”

A cikin wasikar, Naziru ya yi godiya ga masarautar bisa damar da ya samu na yin aikin, wanda a cewarsa ba zai taba mantawa ba a rayuwarsa.

Tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ne ya nada Naziru M. Ahmad Sarkin Waka a shekarar 2018, sarautar da ya rike har zuwa lokacin da ya yi murabus.

Da yake tabbatar da wasikar, Naziru M. Ahmad ya wallafa wasikar a shafinsa na Instagram, inda ya rubuta a kasa cewa, “Alhamdulillahi! Wannan da gaske ne jama’a.”

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya