Da Dumi Dumi

Naziru Sarkin Waka ya yi murabus daga sarautarsa

Sarkin Wakar Sarkin Kano, Alhaji Naziru M. Ahmad ya yi murabus daga sarautarsa ta Sarkin Waka.

A wata wasika da  Aminiya ta gani, Naziru ya aike wa Majalisar Sarkin Kano cewa ya ajiye sarautar ce don kashin kansa, wanda ya ce zai fara aiki ne daga 13 ga wannan watan da muke ciki.

A sakonsa a shafinsa na Instagram, Naziru ya wallafa wasikar, sannan ya rubuta a kasa, “Alhamdulillah. Wannan da gaske ne jama’a.”

Idan ba a manta ba, tubabben Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, ne ya nada Naziru wannan sarauta ta Sarkin Waka, wanda yanzu haka kuma Gwamnatin Jihar Kano ta tube shi daga sarautar ta Kano, inda ta maye gurbinsa da Aminu Ado Bayero.

 

ADVERTISEMENT

 

View this post on Instagram

 

Alhamdulillah. Wannan da gaskene jama’a

A post shared by Naziru Muhammad Ahmad (@sarkin_wakar_san_kano) on

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya