✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Naziru Sarkin Waka ya yi murabus daga sarautarsa

Sarkin Wakar Sarkin Kano, Alhaji Naziru M. Ahmad ya yi murabus daga sarautarsa ta Sarkin Waka. A wata wasika da  Aminiya ta gani, Naziru ya…

Sarkin Wakar Sarkin Kano, Alhaji Naziru M. Ahmad ya yi murabus daga sarautarsa ta Sarkin Waka.

A wata wasika da  Aminiya ta gani, Naziru ya aike wa Majalisar Sarkin Kano cewa ya ajiye sarautar ce don kashin kansa, wanda ya ce zai fara aiki ne daga 13 ga wannan watan da muke ciki.

A sakonsa a shafinsa na Instagram, Naziru ya wallafa wasikar, sannan ya rubuta a kasa, “Alhamdulillah. Wannan da gaske ne jama’a.”

Idan ba a manta ba, tubabben Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, ne ya nada Naziru wannan sarauta ta Sarkin Waka, wanda yanzu haka kuma Gwamnatin Jihar Kano ta tube shi daga sarautar ta Kano, inda ta maye gurbinsa da Aminu Ado Bayero.

 

 

View this post on Instagram

 

Alhamdulillah. Wannan da gaskene jama’a

A post shared by Naziru Muhammad Ahmad (@sarkin_wakar_san_kano) on