Da Dumi Dumi

NCC ta bada wa’adin kwana 10 na rufe katin SIM miliyan 2

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umarci Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) cewa, daga yanzu zuwa ranar 25 ga Satumba 2019 ta rufe katin layukan sadarwa SIM guda miliyan 2.224 wanda ba a yi wa rijista ba daga na’urar sadarwar kasar.

Ministan sadarwa Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ne ya sanar da hakan a ofishinsa da ke Abuja a lokacin da sabbin shugabannin hukumar NCC suka kai masa ziyara.

Ministan ya kara da cewa, bayan cikar wa’adin kwanakin da aka sanar wasu masu amfani da katin layukan sadarwan ba zasu samun damar yin amfani da shi ba.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya