✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NCC ta bukaci kamfanoni su ci moriyar yarjejniyar ciniki ta Afirka (AfCFTA)

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta zaburar da kamfanonin tarho kan su kara kokari wajen ganin sun ci moriyar yarjejeniyar cinikayya ta Nahiyar Afirka  (AFCFTA)…

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta zaburar da kamfanonin tarho kan su kara kokari wajen ganin sun ci moriyar yarjejeniyar cinikayya ta Nahiyar Afirka  (AFCFTA) wacce Najeriya ta sanya wa hannu kwanakin baya.

Hukumar NCC ta ce a matsayin Najeriya na jagora a harkar tarho a kasashen Afirka da ke Kudu da sahara za ta iya samar wa mutanen nahiyar biliyan daya da digo biyu layukan tarho da za su bunkasa hada-hadar cinikayya a nahiyar.

Hukumar ta ce akwai alfanu mai yawa a yarjejniyar, saboda haka ya zama wajibi Najeriya ta shirya wa kalubalen da ke tattare da lamarin.

Bisa la’akari da kasancewar harkokin tarho daya daga cikin muhimman fannonin da nahiyar ta yi yarjejeniyar, Hukumar NCC ta ce akwai bukatar kamfanoni su sanya jari kan sanya kayayyakin aiki don fafatawa a kasuwanni Nahiyar Afirka wanda zai ba su damar samun alfanu  wajen samar da layuka ga mutum biliyan daya da digo biyu.

Da yake jawabi a Legas a taron kwana biyu da ya kare ranar Lahadi, Shugaban Hukumar Gudanarwa ta Hukumar NCC, Sanata Olabiyi Dirojaiye ya ce hukumar ta gano alfanun da yarjejeniyar AFCTA ta zo da shi wanda a cewarsa idan aka yi amfani da shi zai karfafa kasuwar Najeriya.

“A Hukumar NCC mun fahimci cewa yarjejeniyar cinikayya ta Nahiyar Afirka tana nufin yanzu muna da damar fadada ayyukan tarho ga mutum biliyan daya da digo biyu a Afirka. Tare da wannan adadi  da ya hada da matasa wadanda suke kishirwar data da tarho zai ci gaba da karuwa, kamfanoni da masu sanya jari ba su da wata iyaka dangane da hada-hadar kasuwanci. Kamar yadda muka amince da masu sanya jari a kasuwannin Nahiyar Afirka mun san akwai kalubale ba za mu kira shi barazana ba. Kamfanoni da masu zuba jari a harkar sadarwa dole su yaba da wannan dama don tabbatar sun shirya musu. Daga nan kuma akwai bukatar shirya taron wayar da kai,” inji shi

Durojaiye ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da bunkasa aikin masana’antar ta hanyar karfafa  karin jari da damawa da masu da ruwa-da- tsaki kan batutuwan cimma buri tare da tattauna bunkasa bangaren da tattalin arziki.

Da yake jawabi tun farko, Shugaban Hukumar NCC, Farfesa Umar Garba Dambatta ya bayyana cewa bisa la’akari da sanya mambobi 22 na Kungiyar Nahiyar Afirka, yarjejniyar cinikayyar ta zama wata babbar kafar ciniki a duniya ta fannin shigar kasashen, tun lokacin da aka kafa Kungiyar Ciniki ta Duniya (WTO) “Abin da hakan yake nufi shi ne tsarin yarjejniyar AfCFTA  zai canja, inda zai yi wahala ga wata kasa ta zama babbar kafar kasuwanci a Nahiyar Afirka, tunda nahiyar za a rika ganinta a matsayin tsintsiya madaurinki daya a idanun duniya,” inji shi

Dambatta wanda Daraktan Dokoki da Bayar da Hurumi na Hukumar, Muhammed Babajika ya wakilta ya ce an shirya taron ne don a ga yadda za a bunkasa gasa a kan fiye da Dala biliyan 70 ta kasuwar Najeriya a yarjejeniyar kasuwacin nahiyar.

A nasa bangaren, Mukaddashin Daraktan Bai-daya na Yarjejniyar Ciniki ta Najeriya (NOTN), Liman Liman ya bukaci kamfanoni su yi amfani da damar yarjejeniyar AfCFTA.  Ya ce  akwai bukatar sanya ido mai karfi don hana gasa ta rashin adalci a kasuwar. Liman ya bayyana cewa don gogayya a duniya ana bukatar kudi mai yawa a harkar kafa na’urorin tarho daga masu zuba jari a cikin gida da kasashen waje.