Da Dumi Dumi

NCC ta gudunar da taron kara wa juna sani a Jigawa

Don wayar da kan abokan huldar kamfanonin sadarwa da samar da cikakkun bayanai a kan kare hakkinsu Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta shirya taron kara wa juna sani a karamar Hukumar Kazaurea Jihar Jigawa.

Taron kara wa juna sani karo na 42 mai taken ‘Amfanin ilimin sadarwa wajen kare abokan hulda da nufin wayar da kan abokan hulda a kan sanin hakkinsu ta fannin sadarwa.

Daraktar sashin abokan  hulda ta NCC, Misis Felicia Onwuegbuchulam, wanda Mataimakinta, Ismail Adedigba ya wakilta, ta ce, wannan taro an shirya shi ne, da nufin hado abokan hulda a karkara tare da masu kamfanonin sadarwa da kuma hukumar don warware matsalolin da abokan huldasuke fuskanta. Hukumar NCC a shirye take ta amince da  cewa ‘abokin hulda sarki ne’ don haka yana da ’yancin zabin abin da yake so da ’yancin samun ilimi da kuma ’yancin samun tsaro.

Adedigba, ya ce, NCC a shirya hukumar take ta magance matsalolin da abokan hulda suke fuskanta kuma an shirya matakan da za a bi don kauce wa cutar abokan hulda.

A yayin taron an ware bangaren sauraren korafi daga masu kamfanonin sadarwa da abokan hulda masu fuskantar matsaloli a harkokin sadarwa don magance matsalolin da suka gabatar.

ADVERTISEMENT

Hukumar NCC ta shirya tarurruka da dama da nufin wayar da kan abokan hulda da kamfanonin sadarwa. Taron kara wa juna sanin da Hukumar NCC ta shirya na daya daga cikin hanyar da za a iya haduwa da abokan hulda na karkara da masu kamfanonin sadarwa don tattauna hanyoyin magance matsalolin da ake fuskanta a harkar sadarwa, kuma wannan wata hanya ce da abokan hulda za su mori kudaden da suke kashewa a harkar sadarwa tare da samun gamsassun bayanai daga kamfanonin sadarwar da suke hulda da su.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya