✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NCC ta hada gwiwa da Majalisar Dokoki don kafa dokar shafukan sadarwa

Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce, ta shirya don hada gwiwa da Majalisar Dokokin Najeriya don kaddamar da dokar shafukan sadarwa.…

Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce, ta shirya don hada gwiwa da Majalisar Dokokin Najeriya don kaddamar da dokar shafukan sadarwa.

Kwanturolan NCC a shiyyar Kano Malam Tanimu Bawa ne ya bayyana haka a Daura yayin taron ganawar da aka yi da abokan hulda ranar Alhamis. Ya ce, yanayin da ake amfani da shafukan sadarwa na bukatar garambawul a maimakon a ce ana amfani da tsarin don bayyana abubuwan da za su kawo zaman lafiya. Bawa ya ce, manufar shirin shi ne sauraren matsalolin da abokan hulda ke fuskanta tare da bayyana hanyoyin magance matsalolin da nufin inganta harkar. Kwantirolan ya bayyana cewa, babban muradun hukumar shi ne samar da ingancin ayyukan hukumar. Hukumar NCC a cikin shekara 18 ta yi rijistar masu amfani wayar hannu miliyan 162 a kasar nan. “Mun fadada karfin na’urar sadarwa da kashi 22 cikin 100 na karfin ‘data’ daga adadin baya da aka gabatar na kashi 13 cikin 100,” inji shi.

Alhaji Bawa, ya gardadi manyan ‘yan kasuwa a kan sayar da layin way mara rajista da kuma yin rajistar da ba a amince da ita ba wadanda suke bude cibiyoyin bogi don kara wa masu wannan harkar kwarin gwiwa.