Da Dumi Dumi

NCC ta hada gwiwa da sojojin sama don horar da ma’aikata akan ICT

Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta Najeriya (NCC)za ta horar da ma’aikatan Rundunar Sojin Sama a fannin ilimin fasahar sadarwa ta zamani (ICT), kamar yadda manyan shugabannin suka sanar. Shugaban Hukumar NCC Farfesa Umar Garba dambatta da Shugaban Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Iya Mashal Sadikue Abubakar suka bayyana hakan a ranar Alhamis din makon jiya lokacin da ayarin sojojin saman tare shugabansu suka ziyarci ofishin NCC a Abuja.

Farfesa dambatta ya jinjina wa shugaban sojojin saman a kan nasarar da dakarun kasar suke samu na yakar ’yan ta’adda da sauran masu tayar da hankalin jama’ar kasa, ya yi alkawarin taimakon dakarun sojin sama a fannin horarwa a Cibiyar Ilimin Kwamfuta ta Digital Bridge Institute, (DBI) kan fasahar sadarwa ta zamani.

Shugaban NCC ya tabbatar shugaban sojin saman cewa a  shirye suke su bayar da nasu taimakon da cike gurbin da ake samun matsaloli. Mun fahimci akwai nasarorin da ake samu a yakin da ake yi da mayakan Boko Haram a Arewa maso Gabas sannan muna fatan yanayin yankin ya fada zai sake farfadowa nan gaba. Ilimin fasahar sadarwa na zamani na da matukar muhimmanci.

A yayin ziyarar shugaban sojin sama da manyan jami’an hedkwatar sojin saman sun bayyana cewa, rundunar sojin saman na da alaka da fasahar sadarwa don dakile kalubalen tsaro da ake fuskanta a karni na 21 saboda ci gaban fasahar da ake samu. Shugaban sojin saman ya ce, a bangaren jami’an tsaron suna ci gaba da bullo da hanyoyin inganta ayyukan jami’an tsaro wadanda suka hada ilimin fasahar sadarwa na zamanitare da fasahar yaki ta ISR.

A cewar Mashal Abubukar rundunar sojin saman Najeriya ta horar da ma’aikatanta a fannoni da dama cikin shekara uku wadanda ke da dangantaka da fasahar sadarwa a kasashen Amurka da Indiya da kuma wasu horarwar da aka na cikin gida, kuma har yanzu akwai gibin da za a cike ta hanyar hadin gwiwa da Hukumar NCC.

ADVERTISEMENT

Iya Mashal Abubakar ya bayyana wa Shugaban NCC cewa, rundunar sojin saman Najeriya na shirin kaddamar da sansaninta a Bauchi da Zamfara kuma suna bukatar gudunmawar na’urar sadarwa don samun bayanai a yankunan.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya