✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama mutum 186 a Jigawa

Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama mutum 186 da ake zargi da sha ko mu’amala da miyagun kwayoyi a…

Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama mutum 186 da ake zargi da sha ko mu’amala da miyagun kwayoyi a Jihar Jigawa.

Shugabar Hukumar a Jihar Jigawa, Misis Obi Josephine ce ta bayyana haka a ranar Talatar da ta wuce lokacin da take zantawa da manema labarai.

Ta ce masu sha da kuma tu’ammali da miyagun kwayoyi yawansu ya ragu a jihar idan aka kwatanta da bara. Ta ce a bara an kama kimanin mutum 593 ne amma a bana yawansu ya ragu zuwa 186 wanda hakan ya nuna an samu raguwa.

Misis Obi ta nuna takaici kan yadda wadansu manya a kasar nan suke neman a halatta yin amfani da wiwi don biyan bukatun kansu.  Ta ce amfani da wiwi wajen hada magunguna da wasu kasashe ke yi, ba zai yiwu a kasar nan ba, domin irin wiwin da ke kasar nan ta sha bamban da ta sauran kasashen.

“Ba da irin wiwin da ke kasar nan ne ake yin magunguna ba,” inji ta.

Da ta juya game da matsalolin da ke addabar hukumarta a jihar kuwa, ta ce suna fuskantar karancin kudi da ma’aikata da kuma kayayyakin aiki kamar isassun motoci da makamai.

Ta ce batagari kan kai musu hari a duk lokacin da jami’anta suka fita don gudanar da aiki inda hakan ya sa suke daukar ’yan sanda da sojoji da Sibil Defens.

Ta ce duk da rashin isassun kayayyakin aiki da kudi, hukumar tana samun gagarumar nasara wajen yaki da masu sha da fataucin miyagun kwayoyi a jihar.

Daga nan ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tarayya su kawo wa hukumarta dauki a jihar don ganin an tsabtace jihar da kasa baki daya daga batagarin da ke yin mu’amala da miyagun kwayoyi, wanda hakan yake jefa al’umma musamman  matasa cikin mawuyacin hali.

Sannan ta yi kira ga ’yan siyasa su guji yin amfani da matasa wajen ba su miyagun kwayoyi su yi musu aiki musamman a lokutan zabe.  Sai ta shawarci matasa su yi karatun ta-natsu don ganin sun dora rayuwarsu a bisa hanya tagari maimakon rungumar harkar shaye-shaye.