✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Neja za ta iya wadata Afirka da abinci – Osinbajo

Mukaddashin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Jihar Neja tana da damarmaki a harkokin noma wanda za su ciyar da Afirka, don  haka…

Mukaddashin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Jihar Neja tana da damarmaki a harkokin noma wanda za su ciyar da Afirka, don  haka ya ce Gwamnatin Tarayya za ta hada karfi da Gwamnatin jahar wajen bunkasa harkokin noman da zimmar ciyar da fiye da kashi 50 cikin 100 na al’umar Nahiyar Afirka baki daya.

Farfessa Yemi Osinbanjo, ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da bikin bude taron bunkasa harkokin kasuwanci na kwanaki biyu a Minna, babban birnin jahar mai taken, “Habaka Tattalin Arziki A Fannin Sababbin Dabarun Cigaban Noma”.

Mukaddashin Shugaban kasar ya ce tuni suka cimma nasarar tattauna kyakkyawan tsarin da gwamnatin tarayyar da Gwamna Abubakar Sani Bello, don tabbatar da cewa an cimma wannan buri.

“Jihar Neja ta na kashi 10 cikin 100 na yawan murabba’in kasar da Najeriya ke da shi, sannan fiye da kashi tamanin na kasar ta noma ce. Wadannan dam dam guda uku da jihar ke da su da kuma wasu kanana birjik, sun maida jihar zakarar gwajin dafi wajen cimma nasarar karkatar da akalar tattalin arziki ta hanayar samar da kudaden shiga a harkokin noma,” a cewarsa. 

A yayin da yake jawabi tun da farko, Gwamnan Jahar, Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewa noma ita ce sahihiyar hanyar raya tattalin arziki, domin nan da shekaru 20 zuwa 30, kasashen yammacin duniya da suke kera motoci wadanda suke amfani da man fetur za su daina, su maida hankali wajen kera motoci masu aiki da wutan lantarki.