Ministan Aikin Gona Mista Audu Ogbeh ya ce gazawar gwamnatin wajen bayar da kulawar da ta kamata ga makiyaya da kiwon shanu kamar yadda ake yi a sauran kasashen duniya ne yake kawo rikicin da ke jawo kashe-kashen rayuka a tsakanin Fulani makiyaya da manoma.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron da gwamnoni shida da wadansu ministoci da shugabannin hukumomin tsaro suka gudanar kan rikicin manoma da makiyaya a wasu jihohin kasar nan a ranar Litinin da ta gabata.
daruruwan mutane ciki har da mata da kananan yara ne aka kashe a rikice-rikicen da suka ci gaba da aukuwa a akalla jihohin shida.
Rikici na baya-bayan nan ya auku ne a jihohin Benuwai da Taraba da Adamawa da Kaduna.
Minista Ogbeh ya ce, “A shekara da shekaru ba mu yi abin da ya kamata wajen kulawa da bunkasa harkar kiwo a kasar nan ba. Ina bakin cikin in shaida muku cewa a shekara 50 da suka gabata, in ba a baya-bayan nan ba, mun yi abubuwan sosai ga manomin shinkafa da manomin rogo da manomin masara da manomin koko, amma ba mu yi abin kirki ga makiyaya ba, kuma wannan rashin katabus da watsi daga bangarenmu ne ya jawo rikice-rikicen da muke gani a yanzu.”
Ya ce, “A kasashen Turai kowace saniyar da ake kiwo tana samun tallafi na Yuro shida a kullum, ba mu yi komai ga makiyayanmu ba, kuma a sakamakon haka ne harkokinsu suka zama barazana ga sauran manoma.”
Cif Ogbeh ya ce gwamnatin tana shirin bullo da wani shiri da ake kira ‘cibiyoyin kiwon shanu’ a wani bangare na kawo karshen rikice-rikicen. “Akalla za a samar da fili mai girman hekta dubu biyar hade da wadataccen ruwan da fasalin kiwo domin gudanar da hakan.”
Minista Ogbeh ya ce kuma za a samar da tsaro ga cibiyoyin kiwon ta hanyar samar da masu tsaro na zamani, inda ya ce za a hanzarta aiwatar da hakan domin kawo karshen kashe-kashen. “Kuma muna son mu dakatar da makiyaya shanun daga kai-kawo. Za a samar wa shanun ruwa da cikakken tsaro daga kwararrun masu tsaro,” inji shi.
Ya ce ana amfani da cibiyoyin kiwon cikin nasara a kasashen Indiya da Habasha da kuma Brazil.
A wajen wani taro da aka shirya wa ma’aikata da nadaddun ’yan siyasa Minista Ogbeh ya fayyace cibiyoyin kiwon wadanda ya ce sun fi wuraren kiwo na zamani da ake magana girma sosai. Kuma za a gaggauta hakan domin a kawo karshen rikicin manoma da makiyaya.
Cif Ogbeh ya ce, tuni jihohi 16 sun bayar da filayen da za a kakkafa cibiyoyin, inda ya ce, “tsarin ba mai araha ba ne, amma Shugaban kasa ya shaida min da kansa cewa idan muna bukatar taimako daga gare shi zai bayar a kan abin da ya fi kasafin kudin da muke da shi.” Da ya juya kan yawon kiwon shanu Ministan ya ce: “Na san wadansu mutane suna cewa yawon kiwon shanu al’adarmu ce, to amma su sani idan al’ada ta fara kama hanyar zama hadari da za ta jawo yaki a tsakanin mutane a rika zubar da jini da kashe-kashe, akwai bukatar a auna wannan al’ada.”
Ya ce, tunda yawon kiwo a yanzu yana zama abin cutarwa, Gwamnatin Tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa wajen sake fasalinsa ba. “Bai kamata a ci gaba da tafiya da al’ada saboda ita al’ada ce, idan har tana cutar da jama’a za mu yi mata gyara,” inji Ministan.
Taron wanda ya gudana a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Aminiya ta samu labarin an tafka muhawara kan dokar hana yawon kiwo da gwamnonin jihohin Benuwai da taraba suka sanya wa hannu. Kuma majiyar ta ce wani Gwamna ya soki halaccin dokar, inda ya ce za a iya kalubalantarta a kotu kuma a soke ta a karshe. Taron ya tattauna tare da auna hanyoyin da za a kawo karshen rikicin da ke addabar jihohin inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu.
Da yake jawabi kafin a fara zaman sirri na taron, Janar Dambazau ya ce, ya yi Allah wadai da kashe-kashen da ke gudana a tsakanin manoma da makiyayan a jihohin Taraba da Benuwai, inda ya ce tilas ne a dakatar da hakan, tare da gargadin cewa gwamnati ba za ta lamunci tayar da zaune-tsaye ba a kowane bangare na kasar nan. Ya ce, “Halin da ake ciki yana mugun cutar da Arewa da kasar nan baki daya,” inda ya ce, yana iya jawo karancin abinci idan ba a hanzarta magance shi ba.
Da suke tattaunawa da manema labarai bayan kammala taron gwamnonin Taraba da Benuwai sun nace kan cewa za su ci gaba da shirinsu na hana kiwo a jihar.
Gwamnan Jihar Benuwai wanda shi ne ya fara magana, ya ce, wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta gamsar da shi cewa cibiyoyin kiwon da take son gabatarwa sun fi shirinsa na samar da makiyaya ta zamani. Ya ce idan Minista Ogbeh ya gamsar da su za su iya duba hakan, amma a yanzu za su ci gaba da tsarin makiyaya ta zamani.
Shi kuma Gwamna Otorm ya musanta cewa an bullo da tsarin makiyayar zamani a jihar domin a kori Fulani makiyaya daga jihar, inda ya ce za a bar makiyaya su zauna a jihar amma wajibi ne su mallaki makiyayab ta zamani. Ya ce, “Idan muka ga shanu suna yawo a kan hanya, to mun san an sato su ne kuma za mu dauki mataki a kansu.”
Da yake karanta jawabin bayan taron Gwamna Otorm ya ce, taron yana da muhimmanci, kuma ba za a bayyana dabarun tsaro da aka tsara ga jama’a ba.
Ya ce taron ya amince wajibi ne a kare rayukan makiyaya da manoma da kuma dukiyoyinsu, kuma ya kamata a samu hadin hannu a tsakanin gwamnatocin jihohi da Gwamnatin Tarayya wajen magance rikice-rikicen. Sannan taron ya nemi a dakatar da kalaman nuna kiyayya, sannan a dauki rikicin a matsayin wani babban kalubale na kasa. Taron ya kuma amince cewa za a haramta yawon da dabbobi da sunan kiwo ta hanyar bullo da cibiyoyin kiwo da za a samar muku da kayayyakin inganta rayuwa da tsaro, inda ake sa ran fara kaddamar da sun an ba da jimawa ba.
Gwamnonin da suka halarci taron na farko su ne Nasir El-Rufa’i na Jihar Kaduna da Darius Ishaku na Taraba da Tanko Al-Makura na Nasarawa da Samuel Ortom na Benuwai da Mohammed Jibrilla na Adamawa da kuma Abubakar Bello na Neja.
Ministocin kuma sun hada da Cif Audu Ogbe na Aikin Gona da Raya da na Harkokin Cikin Gida Janar Abdulrahman Dambazau sai Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris da Darakatan Janar na Hukumar Tsaron kasa (DSS) Lawal Daura da Babban Kwamandan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSDC), Abdullahi Gana Mohammadu da kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Gona ta Tarayya, Dokta Bukar Hassan.
A wani labarin, tsohon Gwamnan Jihar Abiya Dokta Orji Uzor Kalu ya ce wadansu manyan ’yan Najeriya da suke adawa da yaki da almundahana na Gwamnatin Tarayya ne suke daukar nauyin kashe-kashen da ake yi da sunan rikicin Fulani makiyaya da manoma. Kanlu wanda ya jajanta wa wa iyalan wadanda aka kashe a jihohin Benuwai da Tabraba ya ce, galibin wadanda suke kashe-kashen suna samun goyon bayan ’yan siaysa ne da suke kule saboda Shugaban kasa ya toshe hanyoyin da suke sace dukiyar kasar nan. Ya ce shi m a ya taba samun matsala da irin wadannan mutane lokacin da yake Gwamna bayan da ya hana su sace dukiyar jihar. Ya ce ana samun matsaloli ne a sassan kasar nan ne saboda Shugaba Muhammadu Buhari ya kawo karshen tsofaffin hanyoyin da ake tafiyar da dukiyar kasar nan.
If you are happy to be contacted by a Daily Trust journalist please leave a telephone number that we can contact you on. In some cases a selection of your comments will be published, displaying your name as you provide it and location, unless you state otherwise. Your contact details will never be published. When sending us pictures, video or eyewitness accounts at no time should you endanger yourself or others, take any unnecessary risks or infringe any laws. Please ensure you have read the terms and conditions.