✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Neymar Junior zai yi jinyar mako 10

Shahararren dan wasan PSG Neymar zai yi jinya ta tsawon mako goma. Hakan na nufin dan wasan ba zai samu damar buga dukan wasanni biyu…

Shahararren dan wasan PSG Neymar zai yi jinya ta tsawon mako goma.

Hakan na nufin dan wasan ba zai samu damar buga dukan wasanni biyu na gasar cin Kofin Zakarun Turai ba, inda PSG din za ta kara da Manchester United a watan Fabrariru.

A shekarar 2017 ne Neymar ya koma kungiyar PSG da ke buga Ligue 1 a matsayin dan wasa mafi tsada a duniya a kan Fam miliyan 200.

Dan kwallon ya ji rauni ne a gasar French Cup inda PSG ta doke Strasbourg da ci 2-0.

A wata sanarwa kungiyar ta ce: “Ta tara kwararrun masana a fannin lafiya don su duba lafiyar dan wasan,” kamar yadda BBC ya ruwaito.

“Bayan da masanan suka yi nazari, sun cimma matsaya kan yadda za a yi masa magani,” inji PSG.

Har wa yau sun ce dan wasan ya amince da matakin “Kuma ana sa ran zai koma wasa bayan mako 10,” inji kungiyar.