✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Neymar na kwadayin Real Madrid

Dan wasan Paris St Germain (PSG) na Faransa, Neymar ya ce zai iya komawa kulob din Real Madrid da taka-leda. Dan wasan ayarin Brazil, wanda…

Dan wasan Paris St Germain (PSG) na Faransa, Neymar ya ce zai iya komawa kulob din Real Madrid da taka-leda.

Dan wasan ayarin Brazil, wanda aka saya da tsada fiye da kowa a tarihin kwallon kafa a duniya yana yin jinyar raunin da ya ji a yatsar kafarsa tun a ranar 23 ga  Janairun bana.

An dade ana alakanta Neymar, tsohon dan kwallon Barcelona da cewa zai koma Real Madrid bayan da PSG ta saye shi a shekarar 2013.

Neymar ya shaida wa gidan talabijin na Channel Globo ‘cewa ’Nan gaba, komai zai iya faruwa.’’ a wata tambaya da aka yi masa na yiwuwar komawarsa Madrid don ci gaba da kwallo.