✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Neymar ya naushi dan kallo saboda fushi

Rahotanni daga Faransa sun ce shahararren dan kwallon Brazil Neymar da yanzu  ke buga wa kulob din Paris Saint Germain (PSG) na Faransa kwallo ya…

Rahotanni daga Faransa sun ce shahararren dan kwallon Brazil Neymar da yanzu  ke buga wa kulob din Paris Saint Germain (PSG) na Faransa kwallo ya naushi wani mai goya wa kulob din baya a ranar Asabar da ta wuce.

Al’amarin ya faru ne jim kadan bayan kulob din Rennes ya lallasa na PSG a wasan karshe na cin Kofin Kalubale na Faransa (Coupe de France) a bugun fanariti.

Kafin wasan, PSG ce ta lashe gasar Rukunin Ligue 1 na Faransa.  Kuma wannan  ne karo na 8 a jere da kulob din yake lashe gasar.

A yayin wasan Neymar ne ya zura kwallo ta biyu a raga inda aka tafi hutun rabin lokaci PSG na gaba da ci 2-0.

Bayan an koma wasa ne kulob din Rennes ya farke kwallaye biyun da hakan ya sa aka kara minti 30 daga nan kuma aka yi bugun fanareti.

A bugun fanareti ne kulob din Rennes ya samu nasara a kan PSG.  Ana tashi wasan sai Neymar ya yi kokarin fita daga filin a fusace amma sai wani mai goyon bayan PSG ya rika zolayarsa, kuma hakan ya bakanta wa Neymar rai ya kai masa naushi, har sai da aka shiga tsakani aka raba su.

Alamu sun nuna cewa Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa za ta ci tarar Neymar a kan wannan rashin da’a da ya nuna.

Bincike ya nuna wannan ba shi ne karo na farko da Neymar yake aikata irin haka kuma ake cin tararsa ba.

Na baya-bayan shi ne yadda Hukumar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) ta dage shi a wasanni uku a gasar Zakarun Turai a kaka mai zuwa saboda kalaman batanci da ya yi ga alkalin wasan da ya hura wasan PSG da Manchester United, inda United ta lallasa PSG da ci 3-1.

Akwai dai alamun da suka nuna  cewa Neymar zai bar kulob din PSG a karshen kakar wasa ta bana.