✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NFF ba ta da niyyar korar Kocin Eagles – Amaju Pinnick

A ranar Litinin da ta gabata ce Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) Mista Amaju Pinnick ya tabbatar wa manema labarai cewa hukumarsa ba…

A ranar Litinin da ta gabata ce Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) Mista Amaju Pinnick ya tabbatar wa manema labarai cewa hukumarsa ba ta da niyyar korar Kocin Kungiyar Super Eagles, Gernot Rohr a yanzu.

Shugaban ya ce tun bayan da Aljeriya ta lallasa Najeriya da ci 2-1 a wasan kusa da na karshe a Gasar Cin Kofin Afirka da za a kammala yau yi a Masar, mutane da dama suke kiransa a waya suna neman ya kori kocin.

Sai dai shugaban ya ce bayan sun yi nazari sun gane bai dace a kori kocin a wannan lokaci ba.

“Hasali ma mun yanke shawarar tura shi kulob din Bayern Munich da ke kasar Jamus da zarar an kammala Gasar Cin Kofin Afirka ta bana don ya kara samun horo.  Hakan zai ba koci Rohr damar kara samun kwarewa a harkar horarwa,” inji Pinnick.

Jim kadan bayan Aljeriya ta lallasa Najeriya a wasan Semi Fainal an ruwaito Rohr yana cewa ya cimma burinsa tunda ya kai kungiyar zuwa matakin kusa da na karshe a yarjejeniyar da ya kulla da NFF.

Kocin ya ce baya ga hayewa da kasar zuwa Gasar Cin Kofin Duniya a bara, yanzu kuma ya kai kasar matakin kusa da na karshe a Gasar Cin Kofin Afirka kuma yin haka babbar nasara ce a gare shi.

Sai dai da yawa daga cikin magoya bayan Super Eagles sun yi korafi game da kwarewar kocin wanda hakan ya sa Najeriya ta kasa lashe Kofin Afirka a bana.