✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NFF ta fara zawarcin Moses don ya buga wa Eagles kwallo

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) Mista Amaju Pinnick ya bayyana niyyarsa ta tuntubar tsohon dan kwallon Super Eagles Bictor Moses don ganin ya…

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) Mista Amaju Pinnick ya bayyana niyyarsa ta tuntubar tsohon dan kwallon Super Eagles Bictor Moses don ganin ya shawo kansa ya ci gaba da buga wa Najeriya kwallo.

Bictor Moses ya daina buga wa Najeriya wasa ne jim kadan bayan an kammala gasar cin Kofin Duniya a Rasha a bara.

Ganin yadda gasar cin Kofin Afirka take karatowa ya sa Hukumar NFF ta fara yunkurin shawo kan Moses don ya janye hukuncin da ya yanke na daina buga wa Super Eagles kwallo.

Amaju Pinnick, a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channel TB a ranar Litinin da ta wuce ya ce kwanan nan zai tafi Ingila don ya gana da Moses a kokarin shawo kansa don ya ci gaba da yi wa Super Eagles wasa.

“Zan tattauna da Moses ne ba don ba mu da kwararrun ’yan kwallo a Najeriya ba, amma saboda yana daga cikin ’yan kwallon da za su taimaka mana a gasar cin Kofin Afirka a bana,” inji Pinnick.

Bictor Moses dan shekara 28 ya fara buga wa Najeriya wasa ne a shekarar 2012, kuma yana daga cikin ’yan kwallon Super Eagles da suka lashe Kofin Afirka a shekarar 2013 a Afirka ta Kudu a karkashin horarwar marigayi Stephen Keshi.

Ya buga wa Najeriya wasanni har sau 37 inda ya zura kwallaye 12 a raga.

Yanzu haka yana wasa ne a kulob din Chelsea da ke Ingila.  Sauran kungiyoyin da ya taba yi wa wasa a Ingila sun hada da Wigan Atletic da West Ham United da Stoke City da kuma Liberpool a matsayin aro.