✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NFF ta karrama Samuel Okwaraji bayan shekara 30 da rasuwarsa

Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF) a ranar Litinin da ta wuce ta tuna da tsohon dan kwallon Green Eagles (Super Eagles a yanzu) Samuel…

Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF) a ranar Litinin da ta wuce ta tuna da tsohon dan kwallon Green Eagles (Super Eagles a yanzu) Samuel Okwaraji wanda ya rasu a ranar 12 ga Agustan 1989 shekara 30 da suka gabata yana cikin buga wasa.

Kuma da yawa daga cikin ’yan Najeriya sun tuna da marigayin inda suka yi masa addu’o’i na musamman.

Okwaraji ya rasu ne a lokacin da yake yi wa Najeriya kwallo a wasansu da Angola kan neman hayewa zuwa gasar cin Kofin Duniya na 1990.  Ya rasu a minti na 77 a wasan a filin wasa na kasa da ke Legas, inda ya yanke jiki ya fadi bayan an garzaya da shi asibiti likitoci suka tabbatar ya kamu da bugun zuciya kuma rai ya yi halinsa.

Samuel Okwaraji, wanda kafin rasuwarsa yana karatun digiri na uku a fannin Lauya a wata da ke Rume a kasar Italiya ya yi wa kungiyoyin kwallon kafa da dama wasa irin su AS Roma ta Italiya da Dinamo Zagreb na Kuroshiya da  Stuttgard na Jamus.

Ya rasu yana da shekara 25.

Mahaifiyar dan kwallon ta sha kokawa game da biris din da Hukumar NFF da mahukunta Najeriya suka yi wajen karrama danta Okwaraji bayan ya rasu ne a yayin da yake yi wa Najeriya kwallo. Sai dai a bana NFF da wadansu ’yan Najeriya sun tuna da shi ta hanyar karrama shi.