✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ni ne uban duk ’yan PDP din Jihar Gombe – danjuma Goje

Tsohon Gwamnan Jihar Gombe Sanata Muhammad danjuma Goje kuma jigo a sabuwar PDP ya ce shi ne uban duk wani dan Jam’iyyar PDP a jihar,…

Tsohon Gwamnan Jihar Gombe Sanata Muhammad danjuma Goje kuma jigo a sabuwar PDP ya ce shi ne uban duk wani dan Jam’iyyar PDP a jihar, domin duk wanda ya ci gajiyar jam’iyyar ya samu haka ne sakamakon gwagwarmayarsa da tsayuwarsa har sai da ta kafa gwamnati a jihar a shekarar 3003. Sanata Goje ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a filin jirgin sama na Gombe lokacin da ya je jihar domin ci gaba da shari’ar da ake yi masa bayan gudanar da taron sabuwar PDP a Abuja.

Sanata danjuma Goje wanda ya ce taronsu na sabuwar PDP wadda suka yi a matakin kungiya sun duba yanayin siyasar Najeriya don su ga me za su yi domin su taimaka wa Najeriya a samu ci gaba da dorewar zaman lafiya.
Game da dalilinsa na cewa shi ne uban PDP a Jihar Gombe Sanata Goje ya ce, “Eh ni ne uban PDP a Jihar Gombe tunda ai da ANPP ce take mulki a jihar a shekarar 2003 ne a karkashin shugabancina na jagoranci yaki da ANPP sai da muka kwace mulki daga hannunsu, Gombe ta dawo Jihar PDP, duk wani mai burgar siyasa a Jihar Gombe yana cewa shi dan PDP ne, to karkashina yake. Domin ni na shugabanci wannan rigima har aka kafa gwamnatin PDP a jihar har wasu suke tinkaho suna cewa su ne ’yan PDP yau, babu wani wanda ya fi ni zama dan PDP yau a Jihar Gombe kowane ne shi.”
Sanata Goje ya ce yana cike da farin ciki matuka da ba zai iya bayyanawa ba saboda yadda ya ga mutane sun yi dandazo domin taryarsa, “Manya da yara, tsofaffi da matasa, a gaskiya ban dauka abin ya kai haka ba, domin na zo shari’a ne ba na zo siyasa ba, amma ina kara godiya ga Allah da Ya sa mutanen Gombe suka san na yi musu ayyuka nagari a lokacin da nake Gwamna har ya sa yanzu suka shirya tara ta musamman gare ni, a filin jirgin sama. Ka ga ba na Gwamna kuma na jima ban zo Gombe, amma na yi mamakin yadda na ga dan Adam a wannan wuri wanda duk wasu sharrance-sharrance da ake yi min bai sa jama’a sun yi kasa a gwiwa wajen zuwa su tare ni ba na gode musu kwarai.”
Wakilinmu ya ruwaito cewa a lokacin da Sanata Goje ya isa shinge ’yan sanda na Tumfure sun yi kokarin hana shi shiga garin ganin irin dimbin jama’ar da suke yi masa rakiya, amma daga baya suka bari saboda ya ce zai koma idan ba za a bar shi ya shiga da jama’arsa ba.