✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nijar na shirin samar wa matasa ayyukan yi don su zauna a kasar

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar tare da hadin gwiwar ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da bakin haure, sun shirya wani taron fadakar da matasa a…

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar tare da hadin gwiwar ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da bakin haure, sun shirya wani taron fadakar da matasa a birnin Tawa, inda aka baje kolin ire-iren ayyukan da za su iya yi a cikin kasar, da suka hada da ayyukan hannu da noman rani ko na damina, domin a fitar da tunanin zuwa kasashen Turai, abin da yake jawo rasa rayuka a cikin sahara da kuma teku.

Daraktan Fadar Ministan Samar wa Matasan kasar ayyuka ya ce wannan taron zai ba da damar bunkasa ayyuka ga masu burin bude masana’antu tare da zaburar da matasa su bude nasu ayyukan yi.

Haka ya ce sun fadakar da su game da ayyukan da ake iya yi a cikin kasar, ya ce wannan na da matukar muhimmanci ga gwamnati.

Gwamnan Jihar Tawa, Malam Musa Abdurahamane, ya ce wannan taro yana da matukar muhimmanci ga matasan kasar, saboda samun damar koyon ayyukan yi domin dogaro da kai a cikin kasar, ba sai sun tafi kasashen Turai ba kamar yadda Muryar Amurka ta rawaito.

Wadansu daga cikin matasan sun bayyana jin dadin wannan tsari da aka bullo da shi na koyon ayyukan yi, sun ce lallai matasa ba za su fita su tafi kasashen waje neman wani abu ba, inda suka yi kira da gwamanati ta kara ba su tallafi da kuma goyon baya.

Har ila yau hukumomin Jamhuriyar Nijar sun ja damarar ganin sai yadda hali ya yi, amma za su ci gaba da tallafa wa abokan huldarsu na Turai wajen dakatar da bakin haure zuwa Arewacin kasar.