✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ninkaya a Kogin Fasahar Malam Sa’adu Zungur (2)

A makon jiya GIZAGO (08065576011) ya fara ninkaya ne da nazari cikin faffada kuma zuzzurfan Kogin Hikima da Fasahar Marigayi Malam Sa’adu Zungur, musamman ma…

A makon jiya GIZAGO (08065576011) ya fara ninkaya ne da nazari cikin faffada kuma zuzzurfan Kogin Hikima da Fasahar Marigayi Malam Sa’adu Zungur, musamman ma ta hanyar bitar shahararren wakensa na “Arewa: Jamhuriya Ko Mulukiya? Akwai darussa da suka danganci zamantakewarmu ta yau da kullum a Arewa da Najeriya baki daya. Ga kashi na biyu:

 

Sai mu gode Allah Shi daya,

Don Shi ne Sarkin gaskiya.

 

Ya mallaki dukkan talikai,

Na kwari da tudu da samaniya.

 

Da mutum, aljan da mala’ika,

Dabbar sarari da ta maliya.

 

Mulki, iko, daula duka,

Na ga Sarki Allah Shi daya.

 

Shi Yake ba wanda Ya so duka,

Ya sarautu a lardin duniya.

 

Shi Yake karbe ta ga taliki,

Don ya dandani wahalar duniya.

 

Shi Ka girmama wanda Ya so duka,

Shi Ka sanya wadansu su sha wuya.

 

Shi Ka cusa dare a cikin wuni,

Kuma Ya zaro hasken safiya.

 

Shi Ka rayawar mamaci duka,

Shi Ke kashe mai rai, Shi daya.

 

IkonSa a kan komai yake,

A ruwa da tudu da samaniya.

 

Alwakilu, mu dogara duk garai,

Zahirinmu da boye a zuciya.

 

Mu amince Zai mana taimako,

Na hakka inda majaziya.

 

Malamaina, ’yan uwa da abokan arziki, yau ma za mu ci gaba da ninkaya a Kogin Fasahar Marigayi Malam Sa’adu Zungur, a cikin mashahurin wakensa na Arewa: Jamhuriya Ko Mulukiya? A yau insha Allahu za mu yi nazari ne a cikin baitoci 12 da na tsakuro a sama.

A wadannan baitoci, Malam yana ci gaba da mukaddima ce, yana shimfida a hanyarsa ta warware jigon nasiharsa, shawarwarinsa da fadakarwa ga al’umma, musamman ta Arewa, dangane da abin da ya shafi rayuwarsu, mulki, addini da al’ada. Ya kuduri aniyar yin haka da gaskiya domin jaddada abin da yake na Gaskiya.

A wadannan baitoci 12 da suka gabata, Malam ya fahimtar da mu mene ne Gaskiya kuma wane ne Gaskiya. A takaice dai kamar yadda na fahimta, Malam na nufin Allah Shi ne Gaskiya kuma Shi ne Mahalicci, Mamallakin kowa da komai. Shi ke Hukuncin komai yadda Ya so kuma a duk lokacin da Ya so. Malam ya zayyana mana siffofin Allah sannan ya nuna mana cewa Shi ne Madogararmu kuma Majibancin dukkan lamuranmu. Malam yana jan hankalinmu da cewa mu lizimci gudanar da dukkan al’amuranmu da gaskiya kuma cikin gaskiya.

Wannan mukaddima ko shimfida ta Malam Zungur tana da madogara daga Alkur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW). Allah (SWT) a cikin Suratul Ikhlas (112:1-4) Yana cewa: “Ka ce, Shi ne Allah Makadaici. Allah Wanda ake nufinSa da bukata. Bai haifa ba kuma ba a haife Shi ba. Kuma babu daya da ya kasance tamka a gare Shi.”

Haka kuma a Suratul Mulk (67:3), Allah (SWT) Yana cewa: “Shi ne wanda Ya halitta sammai bakwai, dabako’ki a kan juna, ba za ka ga goggociya ba a cikin halittar (Allah) Mai Rahma. Ka sake dubawa, ko za ka ga wata baraka.”

Abin da na tsinkaya ke nan a lokacin da na gama ninkaya a baitocin nan 12 na Malam Zungur – Duk abin da za mu aikata ko za mu furta, mu nemi yardar Allah a cikinsa kuma mu yi shi da gaskiya cikin gaskiya, domin Allah Shi ne Gaskiya kuma Sarkin Gaskiya.

Bar mu sake duba baitutoci na gaba, kamar haka:

 

Sallama a gare ku sarakuna,

Mun yi niyyar bayyana gaskiya.

 

Addu’armu ga Allah Rahimi,

Ya kiyaye Arewa gaba daya.

 

Muminai da Masihai jumlatan,

Kuma da Arna, dodannin giya.

 

Tutocin Shaihu Mujaddadi,

Goma sha biyu ne Najeriya.

 

Sa Assiddiku Abubakar,

Ga Arewa tana kan shan wuya.

 

Shehu Alkanemi a Yarwa ko,

Za ka yarda a rushe Mulukiya?

 

Hausawa su da Barebari,

Ai amana ce da kilefiya.

 

Shaihu Laminu shi da Mujaddadi,

Sun bar mana girman duniya.

 

Yalla za mu kiyaye har mu bar,

’Ya’yanmu su gaji halaliya?

 

Ya jikokin Shaihunnai biyu,

Sai ku dau tutarku ta gaskiya.

 

Hakki na kabiloli duka,

Na wuyanku, ku sauke lafiya!

 

Daularku a kayin muminai,

Da wasunsu, ta wanye lafiya!

 

Da aminci babu gwagwarmaya,

Babu zalunci da hatsaniya!

 

Kamar yadda muka tsakuro baitocin nan 13 daga mashahurin waken Arewa: Jamhuriya Ko Mulukiya, ya kamata mu fahimci cewa a wajajen 1953 Malam Zungur ya rubuta shi, kimanin shekaru 66 da suka gabata. Kamar yadda taken waken ya nuna, Malam ya ankara da yadda al’amura suka tabarbare a wancan zamani, matsaloli sun yi wa Arewa cacukwi, ga shi kuma an fara kokowar neman ’yancin kan kasa, inda ake kokarin kakaba wa al’umma tsarin mulkin Nasara na Jamhuriya, wanda ta kowace fuska ya bambanta da tsarin Mulukiya.

Jamhuriyya, tsari ne na kasa-daya-al’umma-daya, ba tare da la’akari da al’ada da addini da yanayin kasa ba. A yayin da tsarin Mulukiya kuwa ya ta’allaka da sarakuna, bisa kula da al’ada, addini da yanayin kasa. Domin ya kawo gyara, a samu dawo da al’umma bisa tsarin mulki na gaskiya, wanda zai dace da al’ummar Arewa, shi ya sa Malam Zungur ya bijiro da wannan wake, domin ya zama wani makami na yakin kwatar kai. Haka kuma, Malam ya hango illar da ke tattare da tsarin Jamhuriya, wanda babu shakka zai kassara al’ummar Arewa, muddin aka dabbaka shi a kansu.

Masu iya magana sun ce, sandar da ke hannunka, da ita kake jifa. Kuma kamar yadda wani hadisi na Manzon Allah ya koyar, cewa idan mumini ya ga abin ki, ya kawar da shi da hannunsa, ko da bakinsa ko kuma ya ki abin a zuciya, wanda hakan shi ne mafi raunin imani. Allah bai hore wa Malam mulki ba, amma Ya hore masa baki (alkalami), don haka sai ya yi amfani da shi wajen jan hankalin masu mulki na zamaninsa da ma al’umma gaba daya.

Haka, Malam Zungur bai bude baki sakaka yana magana gatso-gatso yadda ya so ba. Ya yi amfani da maganar Allah wajen isar da sakonsa, kamar yadda Ya bayyana a Suratun Nahli (16:125), inda Yake cewa: “Ku yi kira zuwa ga hanyar Allah cikin hikima da kyautata harshe…” Da wannan hikima, Malam Zungur ya warware jigon da’awarsa.

Malam tare da sallama da ladabi ya fara jawo hankalin sarakunan Arewa, wadanda a lokacin suke rike da daulolin da Mujaddadi Shaihu Danfodiyo ya kafa a  1808, wadanda adadinsu suka kai 12. Daulolin da suka hada da Sakkwato, Kano, Katsina, Zazzau, Borno, Gwandu, Ilori, Adamawa da sauransu. Malam ya ce zai bayyana gaskiya ne, wacce ita kadaice ke saita al’umma zuwa daidai.

A cikin wadannan baitoci, Malam ya nuna irin al’ummar da ke Arewa, wadanda suka hada da Musulmi, Kirista da ma wadanda ba su da addini. Malam ya ce dukkansu amana ne a hannun sarakuna, don haka wajibi ne su kare Mulukiya, domin su ci gaba da mulkin kowa bisa gaskiya da adalci, kamar yadda magabatansu suka gadar musu.

Haka kuma Malam ya jawo hankalinmu cewa kowace kabila da ke Arewa, akwai fahimta da juna, kuma haka ya kamata a zauna cikin amana da gaskiya. Sarakuna su wanzar da mulkin da zai tabbatar da aminci ga al’ummar Arewa, inda kowa zai yi harkarsa ba tare da gwagwagwa ba, sai cikin aminci da salama.

Malam bai gushe ba yana tuna wa magadan Mujaddadi cewa kada fa su manta da gadonsu na gaskiya, na daulolin da ya kafa musu, kada su bari al’amarin ya balbalce. Malam ya ambaci manyan sarakuna, kamar Sarkin Musulmi Assiddiku Abubakar na Sakkwato da Muhammadu Al’amin Alkanemi na Borno.

A cewar Malam, ya dace sarakunan nan su tashi tsaye, su ceto al’ummar Arewa da ke shan wuya, kuma su hango fitinar da ke gabato su ta “Jamhuriya,” wacce idan suka bari za ta zama babbar annobar da za ta lalata daular kakanninsu Danfodiyo da Shaihu Laminu.

Bayan mun gama ninkaya a wadannan baitoci, ’yan uwa ku taya ni taku ninkayar, ta amsa wannan tambayar: Idan muka kwatanta abin da Malam Zungur ya zayyana na matsalolin Arewa a 1953 da kuma abin da muke gani a yau 2019, shin yaya al’ummar Arewa da na Najeriya muke ciki?