✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ninkaya a Kogin Fasahar Malam Sa’adu Zungur (4)

A mako na uku GIZAGO (08065576011) na ci gaba da ninkaya ne da nazari cikin faffada kuma zuzzurfan Kogin Hikima da Fasahar Marigayi Malam Sa’adu…

A mako na uku GIZAGO (08065576011) na ci gaba da ninkaya ne da nazari cikin faffada kuma zuzzurfan Kogin Hikima da Fasahar Marigayi Malam Sa’adu Zungur, musamman ta hanyar bitar shahararren wakensa na “Arewa: Jamhuriya Ko Mulukiya? Akwai darussa da suka danganci zamantakewarmu ta yau da kullum a Arewa da Najeriya baki daya. Ga kashi na hudu:

Ya ku malamaina, abokai, ’yan uwa da abokan arziki, yau ma da ikon Allah za mu ci gaba da ninkaya a cikin kandamin kandamau na fasahar marigayi Malam Sa’adu Zungur. A yau za mu nazarci baituka goma sha daya, kamar yadda na tsakuro su a nan, daga mashahurin wakensa na ‘Arewa: Jamuriya Ko Mulukiya?’

 

Katsinawa, sai ku yi tuntunin,

Umarun Dallaji, mazan jiya.

 

In ji dai kun hangi mutan Gusun,

Masu mai da kasa Jamhuriya?

 

Ai ga ku da gado mai yawa,

Na zumunci, babu hatsaniya.

 

Ga Sarki Alhaji Usuman,

Ya Nagogo idanun duniya!

 

An bar maka nauyi mai yawa,

Allah sa fa ka sauke lafiya!

 

Mu dai ilimi muka tambaya,

Ko a London ko a Arebiya.

 

Yakubu Yakubu na Maigari,

Ya fi karfin ai masa magiya.

 

Arna da Musulmin Bauchi duk,

Sun yi caffa, don su ga gaskiya.

 

Da shirin mulki mai ka’ida,

Na adala, ban da haramiya.

 

Ilimi na sana’a mai yawa,

Da shirin addinin gaskiya.

 

Da shari’ar bin bahasi da kyau,

Babu hanci, ba kuma toshiya.

 

Kamar yadda malamin ya zayyano, har yanzu dai yana kara kambama muhimmancin ilimi a wadannan baitoci. Yana nuna mana cewa babu wani abu mai matukar muhimmanci, maganin kowace cuta da kowace matsalar rayuwa kamar ilimi. Domin kuwa da ilimi ne ake tafiyar da dukkan wani sha’ani na rayuwa. Da ilimi ake mulki kowane iri, na zamani ko na sarauta. Da ilimi ake sana’a ko aiki ko noma a samu nasara. A jigon wadannan baitoci, a takaice Malam yana kara wa al’umma kaimi cewa a tashi a nemi ilimi, domin kuwa da shi ne ake gudanar da zarafofin duniya.

Malam Zungur a matsayinsa na mai tsinkayen al’amura, sahihin mai fadakarwa, bai kyale mutane da gundarin batu ba, sai da ya shata mana misali, ya waiwaya baya ya kawo mana misalin managartan shugabanni magabata, sannan ya zayyana mana yadda suka gabatar da al’amuransu na rayuwa. Sannan ya nemi mu yi koyi da su a tamu rayuwar, domin mu ma mu yi nasara.

Malam ya kama sunan Malam Umarun Dallaji, ya kira shi da lakanin “Mazan Jiya.” Shin ko ka san wane ne Umarun Dallaje? Wannan taliki, babban malamin addinin Musulunci ne, fakihi kuma mai tsoron Allah. Kamar yadda tarihi ya tabbatar, shi ne Sarkin Katsina na farko a Daular Usmaniyya, domin shi ne ya amso tuta daga wajen Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo a shekarar 1807 Miladiyya. Shi ne ya kafa gidan sarautar Katsina na Dallazawa, inda ya yi mulki har zuwa shekarar 1835, wato ya yi shekara 25 a gadon sarauta. Malam Zungur ya ambaci sunan wannan Sarki ne tare da jawo hankalin al’ummar Katsina, domin ya gargade su da su gane abin da suke ciki, tare da nuna musu sharrin tsarin Jamhuriyya da ke tunkararsu.

Malam ya zayyana wa Katsinawa cewa Sarki Umarun Dallaji ya bar musu gadon gaskiya, zumunci da son zaman lafiya da juna. Ke nan ba Katsinawa kadai ba, Malam Zungur yana ishara ga dukkan al’ummar Arewa da su dauki wadannan halaye masu kyau, domin inganta rayuwarsu.

Haka Malam Zungur ya kama sunan Sarkin Katsina, Usman Nagogo, ya doka misali da shi ne domin al’umma su gane tasirin shugabanni na kwarai da shugabanci. Malam ya ce: “Mu dai ilimi muka tambaya, ko a Landan ko a Arebiya.” Hakan na nufin kowane irin ilimi abu ne mai kyau, na zamani da na addini.

Baya ga sarakunan Katsina, Malam ya kama sunan Sarkin Bauchi na dauri, Malam Yakubu, wanda shi ma ba baya ba ne wajen ilimi da iya mulki na gaskiya da adalci. Malam ya nuna mana tasirin shari’a da yadda Malam Yakubu ya gudanar da ita, cikin bin bahasi dalla-dalla kuma da adalci. Kamar yadda ya nuna mana cewa gudun haramun da kyamatar hanci ko toshiyar baki, halaye ne na kwarai da masu mulkin dauri suka assasa, don haka dole ne mu rike su, a zamaninmu, matukar muna son rayuwa mai kyau

Za mu ci gaba