✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ninkaya a Kogin Fasahar Malam Sa’adu Zungur (9)

Wannan shi ne karo na tara da GIZAGO (08065576011) ke ci gaba da ninkaya da nazari cikin faffada kuma zuzzurfan Kogin Hikima da Fasahar Marigayi…

Wannan shi ne karo na tara da GIZAGO (08065576011) ke ci gaba da ninkaya da nazari cikin faffada kuma zuzzurfan Kogin Hikima da Fasahar Marigayi Malam Sa’adu Zungur, musamman ma ta hanyar bitar shahararren wakensa na ‘Arewa: Jumhuriya Ko Mulukiya?’ Akwai darussa da suka danganci zamantakewarmu ta yau da kullum a Arewa da Najeriya baki daya:

Ya jama’a da ke bibiyar sharhin nan ba da gajiyawa ba, a wanann karo za mu dibiya nazarinmu a kan baitoci goma sha biyu ne da muka tsakuro daga mashahurin waken Malam Sa’adu Zungur, na ‘Arewa: Jumhuriya Ko Mulukiya?’ Marigayin dai bai gajiya ba wajen kawo shawarwari da nasiha ga al’ummar Arewa da masu mulkinta. Duk da cewa shekara 66 ke nan da wannan aiki nasa amma har yau tasirin hudubobin nasa na nan daram.

Babban jigon waken nan dai shi ne, a bi Gaskiya, a guje wa Karya. Malam ya fadada darasinsa, inda bai gajiya ba, ya bayyana mana yanayi, ma’ana da siffofin Gaskiya da kuma na Karya. Haka kuma ya bayyana mana bambance-bambancen da ke akwai tsakanin halayen guda biyu. Ya kuma bijiro mana da sakamakon da kowannensu ke samarwa bayan mutum ya aikata su.

Gaskiya ba ta neman ado,

Ko na dadin muryar zabiya.

 

Karya ce mai launi bakwai,

Ga fari da baki ga rawaya.

 

Ga shudi ga kuma algashi,

Toka-toka da ja sun garwaya.

 

Ba ta ’ya’ya sai ko tai fure,

Sai rassa sun fi dubu daya.

 

’Yan Arewa ku daina gaganiya,

Ku rike daularku da gaskiya.

 

Allah Ya kade muku ja’iba,

Ya tsare ku ga sharrin duniya!

 

To, sarakai sai ku yi tattali,

Na adala ban da haramiya.

 

Sai ku hango gemun dan uwa,

Da ya kama wuta da gaganiya.

 

Don ku nemi ruwa ku yi yayyafi,

Kada ku ma naku ya sha wuya.

 

In kun dage kun shantake,

Bisa al’adu na mazan jiya.

 

Za ku rera fadar da-na-sani,

Da na bi jawabin “Gaskiya.”

 

Allah Ya tsare ku fadar haka,

Ya kiyaye Arewa gaba daya.

 

Shin yaya siffar “Gaskiya” take? “Gaskiya ba ta neman ado, Ko na dadin muryar zabiya.” Kamar yadda baitin nan ya nuna, ita gaskiya ba ta da dadin ji, daci gare ta kamar guna, sautinta karfi gare shi, mai kwankwasa zuciya, mai firgita tunanin azzalumi amma kuma mai sanya natsuwa da shiriya ga mai adalci da kyan nufi.

A gefe daya kuma, Malam ya zayyano mana siffofin Karya. Mu duba wannan baiti: “Karya ce mai launi bakwai, Ga fari da baki ga rawaya.” Ke nan ita karya wata dabi’a ce mai daukar hankali, mai kyalkyali da kyan gani. A dandano kuwa, zaki gare ta zakau amma kuma sakamakonta mummuna ne ga jikin dan Adam. Duk da cewa abin sha’awa ce kuma mai dadin aikatawa, sai dai kuma ba ta haihuwar da mai ido.

Gargadin Malam dai shi ne, al’umma su ankara su daure su bi gaskiya kuma su aikata gaskiya a dukkan al’amuransu. Su guje wa karya, su kiyayi aikata ta da furta ta a cikin lamurransu. Wannan ne kawai zai samar musu da kyakkyawar rayuwa mai armashi a duniya da kuma rayuwar gobe Lahira.

Mu dubi baitocin nan biyu: “Yan Arewa ku daina gaganiya, Ku rike daularku da gaskiya. Allah Ya kade muku ja’iba, Ya tsare ku ga sharrin duniya!” Malam na jan hankalinmu al’ummar Arewa, cewa mu daina duk wata gaganiya, mu rike tare da gina daularmu (yankinmu) bisa gaskiya da adalci. Mu daina duk wata kokowar rayuwar karya, marar fa’ida. Mu maida lamurranmu ga Allah – ma’ana, duk abin da za mu aikata ya kasance bisa dokokin Allah. Ba mu kadai ba, hatta shugabanninmu, su ma su kasance masu adalci da gaskiya a mulkinsu. Bayan haka, mu shagaltu da rokon Allah domin Ya raba mu da sharrin duniya.

Gargadi na gaba shi ne, al’umma ta kasance mai kishin kasa. Domin da kishin kasa ne ake kare ta daga sharri kuma da shi ne ake gina ta. Aikin gina kasa babban aiki ne da ya rataya a wuyan kowa, musamman shugabanni su kasance masu jagoranci na kwarai. Su kuma talakawa su kasance mabiya na kwarai bisa girmama shugabanci.

Idan an samu wannan to, lallai an kauce wa haramiya sai gaskiya da adalci su wanzu. A samu ci gaba da karuwar arziki da zaman lafiya. Daula ta tabbata cikin ni’ima.

Mu duba baitocin nan biyu: “Sai ku hango gemun dan uwa, Da ya kama wuta da gaganiya. Don ku nemi ruwa ku yi yayyafi, Kada ku ma naku ya sha wuya.” Malam yana jan hankalinmu da mu dauki darasi kan yadda wasu dauloli suka ruguje, al’ummarsu suka shiga cikin balbalcewa da lalacewa, saboda sun bar turbar gaskiya, shugabanninsu sun saki hanyar gaskiya da adalci, sun kutsa cikin zalunci da haramiya. Malam yana nufin cewa gani ga wane ya ishe mu tsoron Allah. Yadda za mu kauce wa shan wuyar duniya da ta Lahira.

Malam ya ci gaba da gargadi a baitocin nan: “In kun dage kun shantake, Bisa al’adu na mazan jiya. Za ku rera fadar da-na-sani, Da na bi jawabin “Gaskiya.” Allah Ya tsare ku fadar haka, Ya kiyaye Arewa gaba daya.” Ya nuna cewa duk wanda bai ji bari ba, to lallai zai ji hoho. Ma’ana wanda ya ki ji, to ba zai ki gani ba. Ke nan Malam na kira mu amshi gargadi da nasiharsa, yadda za mu guje wa da-na-sani, wato nadama ke nan. Wannan kuwa masu iya magana sun ce keya ce, daga baya take.

Malam ya bi mu da addu’a, cewa Allah Ya kiyashe mu da fadin da-na-sani, Ya kiyaye yankinmu da al’ummarmu gaba daya

Sai dai kuma babban abin takaicin shi ne, kamar mun yi barci, mun shantake. Ba mu ji gargadi da nasihar Malam ba, ga shi a yau muna ta fadin da-na-sani. Mene ne abin yi ke nan? Mu koma baya, mu yi nazari, mu tuba, mu dauki gargadin Malam. Mu gyara lamurranmu, mu tsoraci Allah, mu jefar da karya, mu rungumi gaskiya. Insha Allahu za mu ga canji.