Da Dumi Dumi

NNPC ya gano man fetur da iskar gas a Bauchi

Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya bayyana cewa, an samu danyen man fetur da iskar gas a Barambu da ke kauyen Alkaleri na jihar Bauchi.

Mukaddashin mai magana da yawun hukumar NNPC Samson Makoji, ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a. A ranar 2 ga watan Fabrairun 2019 ne dai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da hakar danyen man fetur a wata rijiya da ke Kogin Kolmani II.

Rahoton na bayyana cewa an haka rijiyar ne da babban inji mai suna ”IKENGA RIG 101” inda aka haka kusan adadin zurfin kafa13,701, kuma an samu mai da iskar gas a matakai daban-daban yayin hakar da aka gudanar.

Share