✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Noman shinkafa: Jigawa ta kulla kawance da China

Kasar China ta kulla yarjejeniya da Jihar Jigawa kan yadda jihar za ta bunkasa noman shinkafa a kokarin gwamnatin jihar na bai wa aikin gona…

Kasar China ta kulla yarjejeniya da Jihar Jigawa kan yadda jihar za ta bunkasa noman shinkafa a kokarin gwamnatin jihar na bai wa aikin gona fifiko da nufin samar da abinci.

Gwamna Badaru Abubakar ne ya sanya hannu kan yarjejeniyar lokacin da jagororin Kamfanin Lee Group suka ziyarci jihar a kwanakin baya a karkashin jagorancin shugaban ayarin, Mista Slorn Yanhoong.

Mista Slorn Yanhoong, ya ce China na bukatar hada gwiwa da Jihar Jigawa, kasancewarta kan gaba wajen  noman ridi a Afirka; kuma ita ce jihar da ta fi samar da ridin da babu algus a nahiyar.

Ya nuna sha’awar kamfanin wajen zuba jari a jihar da nufin habaka noman ridi da taimaka wa manoman jihar,  musamman ta fuskar noma tare da fitar da ridin zuwa China cikin sauki ba tare da haraji mai tsanani ba.

Ya bada tabbacin samun hadin kai tsakanin gwamnatin jihar da kasar China ta fuskar noma da kasuwanci, inda ya  yi alkawarin samar wa jihar irin ridi mafi daraja da kasashen duniya suke bukatarsa, domin raba wa manoma tare da samar da kayan aikin gona da za su taimaka wa manoma wajen bunkasa noma a jihar.

A jawabin Gwamna Badaru Abubakar, ya ce Allah Ya albarkaci jihar da kasar noma mai girman kadada miliyan 2 da dubu 400 kuma dajin da ba a noma shi ya kai fadin kadada miliyan daya da dubu 400. Ya ce ana noma shinkafa da dawa da wake da ridi da alkama da masara da gero da kankana da sauran nau’o’in kayan gona a jihar.

Bayanan da Bankin Duniya ya fitar a shekarar 2018, sun ce Jihar Jigawa ce kan gaba wajen noman shinkafa a cikin jihohin kasar nan 36. Kuma ita ce kan gaba a kamfanoni masu alaka da aikin gona har guda 24 daga cikinsu 10 sun yi fice kan aikin gona.

A cewar Gwamna Badaru, cikin shekara biyar masu zuwa, Jigawa za ta zama sahun gaba wajen noman shinkafa a kasashen Afirka, ba a Najeriya kawai ba. Sai dai ya ce ba za a cimma burin ba sai dole kasar China da jihar sun samar da iri mai inganci ga manoma da kayan aikin gona na zamani, wanda hakan yana daga cikin yarjejeniyar da suka cimma tsakanin jihar da kasar China, domin jihar ta fara yin gwaji kan tsarin da suke bukatar farawa.