✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Noman wake na bunkasa arzikin karamin manomi – Abubakar Bakori

Wake na daga cikin kayan amfanin gona da manoma ke alfahari da shi domin yana kara bunkasa arzikin kananan manoma musamman in sun bi yadda…

Wake na daga cikin kayan amfanin gona da manoma ke alfahari da shi domin yana kara bunkasa arzikin kananan manoma musamman in sun bi yadda ya kamata wajen noma shi.

Malam Abubakar Falalu Bakori, na daga cikin manoman da ke noman wake a yankin Bakori, a Jihar Katsina, ya bayyana yadda yake noman wake da irin ribar da yake samu a lokacin da suke tattaunawa da wakilin Aminiya. “Idan mutum ya fara noman wake, to in aka ga ya bari sai dai rashin jari ko wani abu daga Allah. Ina noman wake ne saboda yana zamo mini ribar kafa. Domin cikin masara nake noma shi, kuma cikin ikon Allah sai ka ga masarar ta zamo tamkar kyauta aka ba ka, saboda takin da za ka zuba wa masarar shi ne waken zai yi amfani da shi. To duk lokacin da za ka yi wa waken noma sai ya zamo tamkar ba a taba noma komai a wajen ba saboda duk ya mamaye wajen,” inji shi.

Malam Abubakar ya ci gaba da cewa, ta fuskar habaka arzikin karamin manomi, wake shi ne kan gaba, domin inda za a sayar da buhun masara a Naira dubu biyu, to shi wake zai Naira dubu uku  zuwa hudu. Kazalika, ya ce, inda za a noma masara buhu 10, za a noma na wake biyar. Sai dai kuma ya ce, “Ana samun wake ne ta hanyar yi masa wahala. Wadansu sukan yi masa noma akalla sau biyu zuwa uku kafin feshin maganin kwari. Shi kuma feshin ana yin sa a lokacin da waken ya fara kurzunu. Sannan kuma duk wanda yake shuka wake cikin masara a nan yankin, to ina tabbatar maka cewa bayan shekara biyu sai ka ji ya biya kudin aikin Hajji domin ribar da zai samu wadda mafi yawanta daga waken  take fitowa. Na shuka wake na samu tsabar wake buhu guda har da wani abu,” inji shi.

Sai dai Malam Abubakar ya ce: “Dalilin da ya sa ba a ganin ana rububin sayen wake a kasuwa shi ne,  ba na amfanin yau da kullum ba ne.”

Manomin ya ce, akwai bambanci kan yadda ake noman wake a shiyyar Kudu da Arewacin jihar, inda ya ce: “A Arewancin Jihar da suka hada da Katsina da wasu yankuna suna noman wake ne cikin shukar gero da dawa da gyada. Kuma ba su cika kula da shi ba sosai, sannan sun fi noma dan arba’in fiye da dan sanyi. Yana da kyau gwamnati ta kara bayar da tallafi kan noman wake, musamman da maganin kwari, domin shi ne jigon samun waken.”

Shi kuwa Shehu wani manomi daga Kaita, shiyyar da ke daya daga cikin yankunan da ke noman wake a Arewacin Jihar, cewa ya yi, sun fi noma wake dan arba’in fiye da dan sanyi saboda shi ne ya fi saurin shigowa kasuwa. “Muna noma duka nau’in biyu amma ba mu ba shi cikakken fili saboda hade-haden da muke yi. Amma hakan bai hana wannan yanki yin suna da tashe a kasuwar wake ba, domin kusan ina iya cewa, daga yankin Kaita ake fara samun sabon wake,” inji shi.

Malam Shehu ya ce, suna fama da karancin maganin feshi da na tallafin gwamnati. “Muna sayen maganin da tsada. Duk da haka, muna samun riba a noman wake,” inji shi.

A shiyyar Mashi, wani manomin mai suna, Hamisu Gyarta cewa ya yi, “Mu a nan Mashi, muna alfahari da noma da kasuwancin wake. Sanin kowa ne cewa, Kasuwar Mashi na daga cikin manyan kasuwannin wake. Kuma wajen noman wake ne. Kuma muna noma waken nan dan sanyi da dan arba’in kuma muna cin moriyarsu. Sai dai kiranmu ga gwamnati shi ne ta dubi harkar noman wake kamar yadda take sa ido a batun noman shinkafa.”

Malam Hamisu ya kara da cewa, wake yana da amfani a jikin mutun fiye da na shinkafa, saboda haka yana da kyau shi ma a ba shi kulawa ta musamman.