Da Dumi Dumi

NSCDC ta kama barayin wayar wutar lantarki da ta kai Naira niliyan 200 a Gombe

Hajiya Altine Sani Umar
Hajiya Altine Sani Umar

Hukumar NSCDC  a Jihar Gombe ta kama wadansu mutum hudu da ake zargin da sace wayar wutar lantarki ta aikin wutar da ake yi daga Gombe zuwa Kashere da aka kiyasta kudinta zai kai Naira miliyan 200.

Da take gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai a hedkwatar hukumar, Kwamandar Hukumar Hajiya Altine Sani Umar ta ce sun kama mutanen ne ta hanyar rahoton sirri da suka samu a garin Tulmi da ke Tumu a kan hanyar zuwa Kashere da taimakon dagatai da jauraban garin.

Hajiya Altine Umar ta ce wadanda ake zargin su shida ne biyu daga cikinsu sun gudu an kama hudu, ta kuma ce suna ci gaba da bincike don gano  sauran wayar wutar lantarkin mallakar Ma’aiatar Makamashi da ta bada aiki mai tsawon kilomita 68.

Kwamandar NSCDC ta kara da cewa tuni hedkwatar ta yi magana da Ma’aiakatar Makamashi ta kasa inda ta ba su umurni su hukunta masu laifin.

Hajiya Altine ta ce shi babban wanda ake zargi da ta’asar, Mista Elojah Electricals shi ne aka samu wayoyin a shagonsa sauran kuma a wajen ajiyarsa inda a nan ne aka kiyasta kudin wayar da cewa ta kai ta Naira miliyan 200.

ADVERTISEMENT

Ta ce tuni hedkwatar ta kammala bincikenta inda ta tura su zuwa kotu.

Sai ta roki al’ummar Jihar Gombe su rika ba su rahotanni masu muhimmanci da za su kai su ga dakile ayyukan batagari a cikin al’umma.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Mista Elojah Electricals cewa ya yi, ya sayi wayar ce daga wajen wani amma bai san cewa ta sata ba ce.

“Ina zaune a shagona sai na ga jami’an Hukumar NSCDC, inda suka ce mu tafi ofishinsu, ban san me na yi ba, da muka je suka ce wai ni mai laifi ne na sayi kayan sata,” inji Elojah.

Share