✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nuna kyama ga baki: Najeriya ta janye Jakadanta daga Afirka ta Kudu

Sakakamakon kai hare-haren nuna kyama ga baki da mutanen Afirka ta Kudu suka kai wa ’yan Najeriya a kasarsu, Gwamnatin Tarayya ta janye Jakadanta daga…

Sakakamakon kai hare-haren nuna kyama ga baki da mutanen Afirka ta Kudu suka kai wa ’yan Najeriya a kasarsu, Gwamnatin Tarayya ta janye Jakadanta daga kasar tare da  kaurace wa taron tattalin arzikin duniya (World Ecomnic Forum) wanda aka fara a shekaranjiya Laraba a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu don nuna bacin rai kan hare-haren.

Janye Jakadan wata alama ce da ke nuna cewa Najeriya na yunkurin yanke alaka da Afirka ta Kudu.

Wata majiyar Fadar Shugaban Kasa ta ce an yanke shawarar janye Jakadan Kabiru Bala ne daga Afirka ta Kudu a wani taron gaggawa da aka gudanar a fadar.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron wanda ya samu halartar Mataimakinsa Yemi Osinbajo da Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama

Tuni Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tura Ministan Harkokin Kasashen Waje Geoffrey Onyeama zuwa Afirka ta Kudu domin kai-dauki ga ’yan Najeriya da ke can. A zantawa da BBC ya yi da wani dan Najeriya mazaunin birnin Johanasbag na Afirka ta Kudu mai suna Ibrahim Bitrus ya bayyana yadda lamarin ya samo asali da kuma halin da ’yan kasashen waje ke ciki, “Rikicin ya samo asali ne lokaicn da wani dan kasar Tanzaniya ya tafi wata unguwa domin sayar da wasu kwaya mai sa maye.

“Kwayoyi ne da matasa kan nika, su sa a cikin taba su sha. To wadansu direbobin motocin tasi a unguwar sun hana yaron zuwa unguwar, amma ya ki.

Da suka kama shi ne sai suka dake shi. Shi kuma sai ya tafi gida ya dauko bindiga ya harbi wani daga cikin wadanda suka doke shi,” inji Ibrahim Bitrus

Ya ce sanadin haka ne aka dora wa ’yan Najeriya wannan laifin, kuma daga nan aka fara kai musu hare-hare.

’Yan Najeriya sun yi ramuwar gayya

Jim kadan bayan aukuwar lamarin, ’yan Najeriya a sasssan kasar nan sun yi gudanar da zanga-zanga tare da kai harin ramuwar gayya  ga kamfanoni da  ma’sana’antu da ake tunanin na mutanen Afirka ta Kudu ne.

An samu rahotanni daga wasu jihohin Najeriya da ke nuna cewa masu zanga-zangar sun je manyan shagunan Shoprites da ofisoshin MTN suna yunkurin lalata su.

Sannan an ga ’yan sandan Najeriya suna kokarin hana masu zanga-zangar kai wa ga masana’antun.