✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NURTW ta fadakar da mambobinta kan zabe a Katsina

kungiyar direbobi ta kasa (N U R T W) reshen Jihar Katsina ta yi taron fadakar da mambobinta a kan zabe a ranar Asabar din…

kungiyar direbobi ta kasa (N U R T W) reshen Jihar Katsina ta yi taron fadakar da mambobinta a kan zabe a ranar Asabar din makon jiya.
A yayin taron wanda aka gudanar a ofishin kungiyar da ke kan titin zuwa Dutsinma da ke cikin garin Katsina an tattauna abin da ya shafi zabe da dokokinsa.
Shugaban kungiyar na jiha kuma Ma’ajin kungiyar a shiyyar Arewa maso Yamma, Alhaji Haruna Mohammed ya bayyana wa shugabannin yankuna da rassan wannan kungiya da suka fito daga kananan hukumomi 34 da ke fadin Jihar  Katsina nauyin da ya rataya a wuyansu wajen fadakar da mambobinsu muhimmancin bin dokoki da ka’idojin zabe.
“Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta nemi hadin kan kungiyarmu domin ganin an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana. Kamar yadda kuka sani, a da kungiya na shiga aikin zaben don kashin kanta ko gayyatar wata karamar hukuma, amma a yanzu abin ya bamban, saboda sanya kungiyar cikin harkokin zaben zundum da hukumar zabe ta yi,.”
Ya ce INEC ta nemi kungiyar a jihohi ta bayar da motoci ga hukumar zabe don aiwatar da ayyukan zaben.
Sakataren kungiyar na jiha Alhaji AbdulRazak Kabara ya ce a yanzu za a samu motoci akalla 20 daga kowane reshe na kungiyar a cikin jihar don gudanar da wannan aikin.
“Ku sani wadannan motoci da za mu bukata a yanzu, za su iya yin kadan ko kuma su yi yawa, amma dai abin da ake bukata shi ne su kasance masu lafiya.” Inji shi.
Sakataren kungiyar mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma Alhaji Ibrahim Yazid ya shaida wa mahalarta taron irin dokokin da aka shimfida a kan wannan aiki, wadanda suka hada da: boye ra’ayin jam’iyya a lokacin da ake aiwatar da wannan aiki na zabe, kaurace wa lika hoton wani dan takara ko nuna goyon bayan wani dan takara a lokacin zabe, ballantana nuna wa wani wanda zai zaba.
Sakataren ya ja hankalin membobin kungiyar su guji karbar umarni daga kowane dan siyasa sai na jami’an hukumar zabe ko wadanda alhakin abin ya shafa musamman jami’an tsaro.