✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obasanjo da Lamido suna butulci ne ga Jonathan – Abba Anas

Tsohon dan Majalisar Tarayya daga mazabar Guri da Kirikasamma da Birniwa a Jihar Jigawa, Alhaji Abba Anas Adamu ya zargi tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo…

Tsohon dan Majalisar Tarayya daga mazabar Guri da Kirikasamma da Birniwa a Jihar Jigawa, Alhaji Abba Anas Adamu ya zargi tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido da cewa tagwaye ne wajen yi wa Shugaba Jonathan butulci tare da yaki da gwamnatinsa da kuma Jam’iyyar PDP.
Alhaji Abba Anas Adamu ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da wakilinmu a Kano, inda ya ce a duk Najeriya babu inda ake mulkin zalunci da danniya kamar Jihar Jigawa saboda a cewarsa babu abin da Gwamna Lamido ke yi illa kama-karya, “amma babu batun dimokuradiyya samsam a Jihar Jigawa,” inji shi.
Ya ce abin ban haushi da takaici gaba daya daga cikin wadanda Jam’iyyar PDP da Shugba Jonathan suka taimaka musu Obasanjo da Lamido da masu rufa masu baya a rigimar cikin gida ta PDP sun juya wa jam’iyyar da Gwamnatin Tarayya baya saboda butulci irin na ’yan siyasa.
Dangane da matsalolin da kasar nan take ciki, ya ce balaifin Shugaba Jonathan ba ne laifin wasu warasa kishin kasa ne da suka haddasa su. Ya ce Oba sanjo na daya daga cikin mutanen da suka sanya kasar nan a cikin matsalolin da take ciki, saboda son zuciya.
Ya ce tun lokacin da aka cire Obasanjo daga shugaban Kwamitin Dattawa na Jam’iyyar PDP yake yi wa gwamnatin Jonathan bi-ta-da-kulli da cin dunduniyarta..
Abba Anas ya ce Obasanjo da Lamido suna yi wa PDP kanshin mutuwa domin su kashe ta, inda ya ce duk kutingwilarsu babu yadda za su yi da Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa domin yana da tabbacin ita ce za ta kafa gwamnati.
Sai ya kalubalaci Gwamna Lamido ya daina sansane-sansane ya fito ya gaya wa duniya cewa ya bar PDP ya ga me zai faru, “yana barazana yana cewa shi malamin siyasa ne, Lamido ba malami ba ne a siyasa har yanzu yana koyon siyasa ce domin babu abin da ya iya illa mulkin kama-karya kamar yadda ya yi kwanan nan a tsayar da ’yan takara na kananan hukumomin jihar 27,” inji shi.