Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Obasanjo ne babbar matsalar kasar nan – Oba Akiolu

Oba na Legas Alhaji Rilwan Akiolu
Oba na Legas Alhaji Rilwan Akiolu

Oba na Legas Alhaji Rilwan Akiolu ya bayyana tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da cewa shi ne babbar matsalar kasar nan.

Oba Akiolu ya bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da littafi kan habaka aikin jarida da tsarin siyasa da wani jigo a Jam’iyyar APC Cif Olusegun Osoba ya rubuta

ADVERTISEMENT

Bikin kaddamar da littafin ya samu halartar jiga-jigan mutane da suka hada da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan da Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai Idris Maje Wase da Jagoran APC na Kasa Sanata Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin Kudu maso Yamma da Gwamnan Jihar Bayelsa Seriake Dickson da tsofaffin gwamnoni da ministoci da sarakunan gargajiya da jakadun kasashen waje da  sauran manyan mutane.

Basaraken ya tabo wani sashi a cikin littafin inda Osoba ya ce Obasanjo ya yaudari gwamnonin tsohuwar Jam’iyyar AD da  Kungiyar Yarabawa ta Afenifere.Sarkin ya ce yana da yakinin cewa tsohon Shugaban Kasar mayaudari ne.

ADVERTISEMENT

Ya ce shi ne babbar matsalar da muke fama da ita a kasar nan, kuma ya ce zai ci gaba da cewa lamba ta daya ta matsalar kasar nan ita ce Obasanjo.

Obasanjo dai bai mayar da martani ga basaraken ba