✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obasanjo ne ya fara lalata jam’iyyun siyasa – Sadeek Musalla

Sakataren Jam’iyyar UPP  ta Kasa, Alhaji Sadeek Ibrahim Musalla ya zargi tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da cewa shi ya fara bata jam’iyyu a Najeriya…

Sakataren Jam’iyyar UPP  ta Kasa, Alhaji Sadeek Ibrahim Musalla ya zargi tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da cewa shi ya fara bata jam’iyyu a Najeriya a lokacin da yake  mulkin kasar nan. Alhaji Sadeek Musalla ya bayyana haka ne, lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya a garin Jos na Jihar Filato.

Ya ce gaskiyar magana tsohon Shugaban Kasa Obasanjo ne ya fara bata siyasa a Najeriya. Domin a lokacin da yake kan mulki ne ya fara raina jam’iyyar da ta dora shi  a kan mulki, ya rika cire shugabanin  jam’iyyar na kasa  a duk lokacin da ya ga dama. Kuma ya karbe karfin jam’iyyar, ya zamanto shi ne yake mulkin jam’iyyar maimakon shugabanta.

Ya ce wannan ne ya rusa dajarar jam’iyya a kasar nan, ya zama shugabannin jam’iyya ba su da wani daraja a wajen shugabanni, tun daga kan Shugaban Kasa har zuwa kan gwamnoni. “Domin  Obasanjo ya mayar da jam’iyya ta zama ’yar kallo kan abubuwan da suke tafiya. Don haka dole ne a samu rigingimu kan yadda Shugaban Kasa da  gwamnoni suke zabar abin da ya kamata a yi, kan jam’iyyu a kasar nan. Don haka gwamnoni suka tsoma baki kan wadanda aka zaba a zabubbukan da aka gudanar a kasar nan,” inji shi.

Alhaji Sadeek ya ce yadda jam’iyyu suka gudanar da  zabubbukan tsayar da ’yan takara a ’yan kwanakin nan, zai sanya mutane da dama su bijire wa ’yan takarar da jam’iyyunsu suka tsayar a zaben kasa baki daya, su koma  su zabi ’yan takarar da wasu jam’iyyun suka tsayar.