✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Obasanjo ya tattauna da shugabannin Kungiyar Fulani

A yanzu haka Kungiyar Fulani makiyaya ta Gan Allah Fulbe (GAFDAN),  nayin taro da tsohon shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo a Abeokuta babban birnin jihar…

A yanzu haka Kungiyar Fulani makiyaya ta Gan Allah Fulbe (GAFDAN),  nayin taro da tsohon shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo a Abeokuta babban birnin jihar Ogun taron na da alaka da matsalar tsaro da halin da Fulani makiyaya ke ciki inda ake alakanta su da aikata miyagun laifuka da suka  hada yin garkuwa da mutane da aikata wasu laifuka a yankunan Kudu maso Yamma.

An gudanar da taron ne a dakin karatu na Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) da ke Oke – Mosan, a Abeokuta babban birnin jihar Ogun.

A cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban kungiyar Fulani ta GAFDAN na kasa, Alhaji Sale Bayari, da sauran wakilan kungiyoyin Fulani daga Kudu maso Yamma da wakilan jihohin Kogi da Kwara.

Sauran sun hada da: Kakakin kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere, Yinka Odumakin da Mista  Dayo Adewole dan tsohon Ministan lafiya Farfesa Isaac Adewole, wanda aka yi garkuwa da shi aka sako shi kwanan nan a Oyo.