✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Obaseki ya bayyana a gaban kwamitin tantance ‘yan takara

Gwamnan Jihar Edo Godwwin Obaseki ya bayyana a gaban kwamitin tantance ‘yan takarar zaben fidda gwanin gwamnan jihar na sabuwar jam’iyyarsa ta PDP a Abuja.…

Gwamnan Jihar Edo Godwwin Obaseki ya bayyana a gaban kwamitin tantance ‘yan takarar zaben fidda gwanin gwamnan jihar na sabuwar jam’iyyarsa ta PDP a Abuja.

Kwamitin Hon. Kingsley Chinda na tantance Obaseki ne domin shiga takarar washegarin ranar da Gwamnan ya koma jam’iyyar.

Obaseki ya shigo PDP wadda ta ba shi damar neman takara ne bayan tsohuwar jam’iyyarsa ta APC ta hana shi.

Bayan shigowarsa PDP a kurarren lokaci jam’iyyar ta kara dage zaben fidda gwanin zuwa Alhamis 25 ga watan Yuni.

Ana zargin hakan na da nasaba da kokarin ba gwamnan damar kintsawa domin zaben da ke tafen ne.