Da Dumi Dumi

OJB Jezreel na bukatar N16m don dashen koda

Mai shirya fina-finai kuma mawaki a Kudancin Najeriya, Babatunde Jezreel Okungbowa, wanda aka fi sani da lakanin OJB yana kwance magashiyyan a wani asibiti da ke Legas, yana fama da ciwon koda.
Kamar yadda kafar watsa labaran ’yan fim da mawaka ta intanet, OMG ta ruwaito, mawakin yana bukatar zunzurutun kudi har dala 100,000 (kimanin Naira miliyan 16) domin yi masa aikin dashen koda.

Share