Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Okereke dan kwallon U-23 ya sanya hannu a kwantaragin Naira biliyan 3 a Beljiyam

Dan qwallon Najeriya David Okereke
Dan qwallon Najeriya David Okereke

Dabid Okereke dan kwallon Najeriya na Kulob din U-23 ya samu nasarar sanya hannu  a kulob din Club Brugge na Beljiyam kan kwantaragin shekara 4 a kan Yuro miliyan 8 (kimanin  Naira biliyan 3 da miliyan 323).

Kulob din ne ya bayyana haka a shekaranjiya Laraba a shafin sadarwarsa na Twitter.  Kulob din ya ce wannan cinikin dan kwallo mafi tsada da kulob din ya yi a shekaru 8 da suka wuce da hakan ya sa Okereke ya kafa sabon tarihi.

ADVERTISEMENT

Dabid Okereke yana kwallo ne a kulob din matasa na Spezia da ke wasa a Rukunin B na Italiya kuma ya samu nasarar zura kwallaye 10 sannan ya taimaka wajen zura kwallaye 12 a raga a wasanni 33 da ya yi wa kulob din a kakar wasan da ta wuce.

Dan 21 Okereke zai maye gurbin dan asalin Brazil Wesley Moraes ne da ya canja sheka daga kulob din zuwa Aston Billa na Ingila.

ADVERTISEMENT

Ana sa ran Okereke zai hadu da dan Najeriya da ke wasa a can mai suna Dennis Bonabenture da wadansu ’yan kwallo 6 da suka fito daga kasashe daban-daban a Nahiyar Afirka.

’Yan asalin Afirka da ke wasa a kulob din na Club Brugge sun hada da Krepin Diatta da Amadou Sagna daga Senegal da Odilon Kossounou daga Kwaddebuwa da Sofyan Amrabat daga Maroko da Marbelous Nakamba daga Zimbabwe da kuma Clinton Mata dan asalin Angola.

Tsohon dan kwallon Super Eagles Daniel Amokachi ya taba buga kwallo a kulob din na Club Brugge na Beljiyam.