✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Onnoghen: Dakatarwa  ba kora ba ce

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Shugaba Buhari ya dakatar da Babban Jojin Najeriya Mai shari’a Walter Onnoghen daga aiki tare da nada Mai shari’a …

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Shugaba Buhari ya dakatar da Babban Jojin Najeriya Mai shari’a Walter Onnoghen daga aiki tare da nada Mai shari’a  Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin mai rikon mukamin  Babban Jojin Najeriya.

Sai dai kuma kamar yadda aka zata wannan matakin da Shugaba Buhari ya dauka ya tayar da kura domin al’amarin ya haifar da muhawara mai zafi a tsakanin ’yan Najeriya masu goyon matakin da masu sukarsa.

Shi dai Shugaba Buhari ya ce, ya dauki wannan mataki ne domin bin umarnin Kotun Da’ar Ma’aikata (CCT) wadda ta umarce shi ya dakatar da Mai shari’a Onnoghen daga mukaminsa ya nada wanda ya fi girman mukami a Kotun Koli a matsayin Babban Jojin har sai kotun ta yanke hukunci kan karar da aka kai Mai shari’a Onnoghen gabanta na rashin bayyana wasu kadarorinsa.

Sakamakon haka ne al’ummar kasar nan suka kaure da muhawara, wadansu na cewa Shugaba Buhari ya yi daidai, wadansu na cewa ya wuce iyakarsa domin tsarin mulki bai ba shi damar yin haka ba.

Muhawarar da ake yi dai ita ce wai Shugaba Buhari bai isa ya kori Mai shari’a Onnoghen ba sai tare da izinin Majalisar Dattawa kuma ba Kotun Da’ar Ma’aikata za a kai kararsa ba, Majalisar Kula da Alkalai (NJC) ya kamata a kai kararsa.

Wannan lamarin ya jawo tayar da jijiyoyin wuya wanda ya sa har Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta bayar da umarni ga ’ya’yanta cewa su kaurace wa kotunan kasar nan na kwana biyu a wannan mako domin nuna bacin ransu ga abin da Shugaban Kungiyar ya kira karan-tsaye ga bangaren shari’a a kasar nan.

Haka su ma gwamnoni da dattawan yankin Neja-Delta, yankin da Mai shari’a Onnoghen ya fito, duk sun nuna bacin ransu da taba dansu da aka yi.

Sai dai kuma wata kungiyar matasan yankin Neja-Delta ta bukaci Onnoghen ya je kotu domin ya kare kansa, ta ce babu wani tunzuri da ’ya’yanta za su yi domin an tuhume shi da tara dukiyar haram. Tana mai nuni da cewa a lokacin da yake wadaka a cikin dukiyar da ya tara ta hanyar da ba ta dace ba ai ya manta cewa shi dan yankin Neja-Delta ne domin babu wani abin a-zo-a-gani da ya yi wa al’ummar yankin, sai yanzu da liki yake neman tashi ne ake son mutanensa su mara masa baya.

Wannan al’amari da ya faru ya sanya wadansu sun yi ta kokarin ganin sun shigo da batun addini da kabilanci, amma ga dukan alamu kan ’yan Najeriya ya waye game da batun domin sun ki yarda a cusa musu wannan ra’ayi.

Shi kansa fitaccen lauyan nan Femi Falana a wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin ta ‘Channel’ ya nuna cewa kamata ya yi Mai shari’a Onnoghen ya sauka daga mukaminsa da kansa, a mutunce ba sai an tilasta masa ba, domin ya kare mutuncinsa, inda Femi Falana ya kawo misalai a ciki da wajen kasar nan da manyan mutane suka sauka daga mukamansu saboda zarginsu da aka yi da aikata ba daidai ba.

Wadansu masana sun nuna cewa Shugaba Buhari bai isa ya sauke Mai shari’a Onnoghen shi kadai ba sai dai tare da Majalisar Dattawa, amma Fadar Shugaban Kasa ta ce ta dakatar da Onnoghen ne ba korarsa ta yi ba. Tsarin mulki ya haramta wa Shugaban Kasa korar Babban Jojin ne, amma bai hana shi dakatar da shi domin yin bincike ba, amma da yake an sanya batun siyasa a cikin lamarin sai aka kawar da kai daga wannan bayani aka koma ana ta suka saboda an taba shafaffe da mai. Da a ce dan wani bangare na kasar nan ne ya yi laifin da ake zargin Onnoghen da shi da an dade da korarsa har ma a tura shi gidan yari kuma babu wanda zai yi magana.

Yanzu dai ruwa ya kare wa dan kada bai gama wanka ba, Mai shari’a Onnoghen dai a shekarar 2013 shi ya jagoranci shari’ar da ta bai wa Kotun Da’ar Ma’aikata damar sauraron karar da ta shafi da’ar ma’aikatan gwamnati ita kadai, amma yanzu da hukuncin da ya yanke a baya ya shafe shi sai ake ta kokarin canjawa.

Kamata ya yi kungiyar lauyoyi ta taimaka wajen tabbatar da bin doka, maimakon ta kawar da kanta daga zargin da ake yi wa Mai shari’a Onnoghen na tara dukiyar haram tare da boye ta, kamata ya yi ta bi diddigin tuhumar da ake yi masa idan ya yi laifi ta tabbatar an hukunta shi kamar yadda doka ta tanada, idan kuma ba ya da laifi a wanke shi.

Domin yaki da cin hanci da rashawa da ake yi ba zai taba samun nasara ba, sai da taimakon masu shari’a, matukar akwai bara-gurbi a cikin alkalai to za a rika fuskantar matsala, domin idan an kama wani ya wawure dukiyar jama’a aka kai shi kotu don a hukunta shi idan ya ba alkalin wani yanki na abin da ya wawure sai ya wanke shi daga laifin a sallame shi.

Kasancewar Mai shari’a Onnoghen babban mai shari’a na kasa baki daya, ya kamata ya nuna misali ga kowa cewa babu wanda ya fi karfin a hukunta shi komai matsayinsa, amma bai kamata a ce, ba za a taba Onnoghen ba saboda shi babban mutum ne a kasar nan. Idan an yi haka an nuna cewa dokokin da ake yi domin marasa galihu ne kawai ban da shafaffu da mai. Kuma yin haka ba zai haifar wa kasar nan da da mai ido ba.